Wata sabuwa: Yadda 'yan bindiga sun sace wasu daliban ajin 'Nursery'
- Wasu 'yan bindiga sun sace daliban makarantar kasa da firamare a wani yankin jihar Ondo
- Lamarin ya faru ne a daren Juma'a, inda aka sace yaran biyu tare da motar mahaifiyarsu
- Rahotanni daga rundunar 'yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma ana aiki akai
Ondo - Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu daliban makarantar kasa da firamare a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.
Jaridar Vanguard ta rahotocewa sace yaran da har yanzu ba a san ko su waye ba ya faru ne a yankin Leo, cikin garin Akure da misalin karfe 8 na daren Juma'a.
Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwar sun bi mahaifiyar yaran ne har gida.
Sun sace yaran ne lokacin da mahaifiyar su ta sauko daga mota don bude kofar gidan ta.
An shiga halin fargaba a sansanin NYSC da ke Zamfara yayin da ‘yan bindiga suka sace masu yiwa kasa hidima
‘Yan bindigar sun gudu da yaran a cikin motar mahaifiyar kirar Toyota Camry mai launin toka.
An tattaro cewa lokacin da mahaifiyar yaran ta dawo bayan ta bude kofar ba ta sami abin hawa da yaran ba.
A lokacin da ta gane ta fara neman taimako, sannan 'yan bindigar sun gudu da yaran yayin da kawai hasken bayan motar ake hangowa 'yan mitoci daga inda aka ajiye ta.
Har yanzu masu garkuwar ba su tuntunbi iyayen yaran ba.
Majiyoyi sun ce wannan abin takaici ya haifar da damuwa a duk fadin babban birnin jihar yayin da iyayen yaran suka kai rahoton lamarin a ofishin 'yan sanda.
The Cable ta rahoto cewa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Funmi Odunlami ta tabbatar da sace yaran biyu na ajin kasa da firamare da satar motar mahaifiyar su.
Ta kara da cewa jami'an binciken 'yan sanda sun fara bincike a kan lamarin kuma sun ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a saki yaran ba tare da jin rauni ba.
'Yan bindiga sun kira wayar wani a coci, ya fito sun bindige shi sun gudu
A wnai labarin, Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wani wakilin kamfanin gidaje da ke Ilorin mai suna Sina Babarinde.
Babarinde, memba ne na Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), an harbe shi ne yayin bauta a cocin Living Word Parish da ke hanyar Basin, Ilorin, PM News ta ruwaito.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya ce lamarin ya faru ne yayin da ake gudanar bautar cocin na RCCG da misalin karfe 7 na safe.
Asali: Legit.ng