Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu

Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu

  • A yau ne za a ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu, an dasa jami'an gwamnati a harabar kotu
  • An ga jami'an DSS, 'yan sanda da sojoji duk a harabar kotun da kuma hanyoyin shiga kotu
  • An dage karar Nnamdi Kanu a baya bisa wasu dalilai, wanda yau ne za a ci ga daga inda aka tsaya

Abuja - Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, an girke jami’an tsaro da yawa a babbar kotun tarayya da ke Abuja don shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra ta IPOB.

An ga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar sojan Najeriya da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suna gadin kowace kofar shiga kotun da titunan da ke shiga ginin kotun.

Ba a bar 'yan jaridar da sunayensu ba sa cikin jerin shirye-shiryen ba a kusa da harabar kotun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An daure dalibai 19 da aka kama sun shiga kungiyar asiri a Jami’a bayan doguwar shari'a

Ma'aikatan kotun da suka isa cikin motocin bas an sanya su a layi kuma an bincike su kafin su shiga harabar.

Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja domin jin shari’ar Nnamdi Kanu
Shugaban IPOB Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Yuni, an kama Kanu aka kawo shi Najeriya don fuskantar shari'a bayan kejewa beli a 2017.

Kwanan nan gwamnatin tarayya ta sake shigar da sabbin laifukan da ake tuhumar sa da su.

Yanzu haka za a sake gurfanar da shugaban na IPOB din bisa tuhume-tuhume bakwai da laifuka biyar da a baya yake amsa su, wadanda suka hada da aikata cin amanar kasa da ta’addanci.

Gwamnatin Buhari ta ce bata gama da Igboho ba, akwai sabbin tuhume-tuhume a kansa

Biyo bayan da wata kotu a jihar Oyo ta umarci a bai wa Sunday Adeyemo (Igboho) Naira biliyan 20, gwamnatin tarayya ta yi nuni da yiwuwar daukaka kara kan hukuncin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: FG ta mika sabbin korafi 7 kan Nnamdi Kanu a gaban kotu

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya Abubakar Malami, ya shaida wa manema cewa gwamnati na da damar daukaka kara kan hukunci ko kuma ta shigar da sabon tuhuma kan dan awaren Yarba Sunday Igboho, rahoton Premium Times.

Ya bayyana haka ne a yau Alhamis, 23 ga watan Satumba, 2021. Malami ya yi bayanin cewa a cikin yanayin yin biyayya ga umarnin doka akwai wasu hakkoki da bukatun da ke hannun gwamnati, Punch ta kara da cewa.

FG ta ki halartar kotu don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta

A wani labarin, Babbar kotun jihar Abia a ranar Talata ta dage sauraron karar da ta shafi jagoran IPOB da aka tsare, Nnamdi Kanu zuwa 7 ga Oktoba, 2021, Punch ta ruwaito.

Alkalin kotun, Jastis KCJ Okereke, ya dauki wannan mataki ne yayin da fg da wasu mutane biyar da ake kara a shari’ar suka gagara gabatar da bayanansu kan karar da Kanu ya shigar gaban kotun, inda yake kalubalantar take hakkin sa da Gwamnatin Najeriya ta yi.

Kara karanta wannan

Kungiya za ta yi shari’a da Buhari, Ministoci 2 a kan yunkurin Gwamnati na sa ido a Whatsapp

A cikin karar mai lamba HIH/FR14/2021, wadanda ake kara sun hada da Gwamnatin Tarayyar Najeriya (1), Babban Lauyan Tarayya (2), Babban Hafsan Sojoji (3), Sufeto Janar na 'Yan sanda (5), ​​Darakta Janar , Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (7) da wasu manya uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.