Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Sace Matafiya 13 a Jihar Neja

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Sace Matafiya 13 a Jihar Neja

  • Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun tare mota sun sace fasinjoji 13 a jihar Neja
  • Monday Kuryas, kwamishinan yan sandan Neja ya tabbatar da afkuwar lamarin
  • Kuryas ya roki al'umma su taimakawa rundunar da bayanai da zasu taimaka a kama yan bindigan

Jihar Neja - Rundunar 'yan sandan jihar Niger, a ranar Laraba ta ce yan bindiga sun sace matafiya 13 a kauyen Konar Barau da ke karamar hukumar Rafi a jihar Niger.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kwamishinan yan sandan jihar Niger, Monday Kuryas ne ya bayyana hakan yayin hira da NAN a Minna, babban birnin jihar.

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 13 a Jihar Neja
Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya 13 a jihar Neja. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

A cewar Kuryas, DPOn 'yan sanda na Zungeru ya bada rahoton cewa wani Mubarak Idris na kauyen Kwanawa, jihar Sokoto ne ya sanar da yan sanda afkuwar lamarin misalin karfe 3.30 na rana.

Idris, wanda aka gano cewa shine direban mota bas mai lamba LGT 12 XWX, ya dako fasinjojin daga Yauri jihar Kebbi ne a lokacin da lamarin ya faru.

Daily Trust ta ruwaito cewa matafiyan, mafi yawancinsu masunta, suna kan kan hanyarsu ta zuwa Yenagoa a jihar Bayelsa ne a lokacin da aka kai musu harin.

Yan sanda sun ce Idris ya bada rahoton cewa a lokacin da suka isa Konar Barau da e hanyar Tegina-Minna ne wasu da ake zargin yan bindiga ne sanya da kayan sojoji suka kaiwa motarsu hari suka sace fasinjoji 13 da karen mota.

Direban ya kuma kara da cewa 'yan bindigan sun raba shi da kudinsa har N131,500.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da barkonon hayaki

Kwamishinan 'yan sanda ya nemi al'umma su taimaka musu da bayanai

Da ya ke magana kan lamarin, kwamishinan yan sandan ya ce tuni an fara farautan 'yan bindigan.

Ya kuma yi kira ga mazauna garin su taimakawa rundunar da bayyanai masu amfani da zai taimaka a kama masu laifin.

Ya ce:

"Muna kira ga mutane su taimaka da bayanai masu amfani da zai taimaka a kama bata garin a jihar.
"Muna yin duk mai yiwuwa don ganin mun tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar da ke karkashin yankin mu.
"Abinda muke so daga al'umma shine bayani mai amfani da zai taimaka mana sanin inda suke tafiya don mu dauki mataki."

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda 'yan sanda suka yi ram da masu zanga-zanga a Lekki Tollgate

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164