Pandora Papers: An bankado yadda alkali a Najeriya ta mallaki kadarori a London
- Bincike ya bankado yadda mai shari'a Stella Ogene, tsohuwar alkalin kotun daukaka kara ta gargajiya a Delta ta mallaki wasu kadarori a London
- An gano cewa mai shari'ar ta tuntubi masu adana dukiyar sirri a London inda suka bude mata kamfanin mai da sunan Assete Media Limited
- Bayan wata hudu, kamfanin ya siya tamfatsetsen gida a birnin London, wanda mai shari'ar ta musanta duk da takardu da aka gani
Binciken Pandora Papers ya bankado kadarorin wata tsohuwar alkali ta kotun daukaka kara ta jihar Delta, Mai shari'a Stella Ogene da ke London.
Kamar yadda takardun da Premium Times ta fitar, Ogene wacce a halin yanzu ta yi ritaya, ta mallaki wasu kadarori a London wanda ta siya ta wani kamfanin mai mallakin ta.
Takardun da Premium Times ta samo sun nuna yadda Mai shari'a Ogene ta samu wani kamfanin adana dukiya mai suna Cook Worldwide wanda ke da ofishi a Panama wanda Chike Obianba ke shugabanta.
Kamar yadda takardun suka nuna, Cook Worldwide ta yi aikin gaggawa kuma an samar da kamfanin Assete Media Limited a ranar 7 ga watan Satumban 2009 wanda Ogene ta zamanta, mamallakiya, darakta kuma sakatariyar kamfanin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Cook Worldwide sun yi hayar Mayfair Trust Group Limited, wani kamfanin kafa kamfanonin mai na Seychelles wanda ya taimakawa Ogene wurin kafa Assete Media Limited a Seychelles, takardun suka bayyana.
An tuntubu mai shari'a Ogene
Jaridar Premium Times ta tuntubi Ogene amma ta musanta alakarta da kamfanin Assete Media Limited, sai dai daga bisani ta aminta bayan an nuna mata shaidun takardu.
Ta ce "Ba ni ce darakta ba. Kawai ina da hannun jari ne. A takardun da kuka gani na rubuta, tsofaffi ne kuma akwai takardun shaidar hakan."
Takardun sun kara da bayyana cewa, a watan Fabrairun 2010, bayan watanni hudu da kafa kamfanin man, Assete ya siya wata kadara a London mai adireshi 2 Old Rectory Gardens, Edgware HA8 7LS, UK.
Terere: Yadda Bishop Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa
A wani labari na daban, shugaban cocin Living Faith Worldwide wanda aka fi sani da Winners Chapel International, Bishop David Oyedepo, an bayyana shi daga cikin 'yan Najeriya da suka kafa kamfanoni a tsibirin Turai na Virgin.
Premium Times ta ruwaito cewa, sunan Oyedepo ya bayyana a cikin takardun Pandora wanda kungiyar 'yan jarida ta International Consortium of Investigative Journalists (ICIJ) suka jagoranta.
Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Peter Obi, Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da na jihar Osun duk sun bayyana a cikin 'yan siyasan da suka washe kudin kasa suka adana a Turai.
Asali: Legit.ng