Terere: Yadda Bishop Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa

Terere: Yadda Bishop Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa

  • Daga cikin wadanda ke handamar dukiya suna auna ta kasashen ketare, an gano Bishop David Oyedepo
  • Fitaccen malamin addinin kirista kuma shugaban Living Faith Worldwide ya bude kamfani a Turai a shekarar 2007
  • Shi da 'ya'yansa maza 2 ne shugabannin kamfanin, shi da matarsa na da hannun jari kashi talatin yayin da 'ya'yansa ke da kashi goma-goma

Shugaban cocin Living Faith Worldwide wanda aka fi sani da Winners Chapel International, Bishop David Oyedepo, an bayyana shi daga cikin 'yan Najeriya da suka kafa kamfanoni a tsibirin Turai na Virgin.

Premium Times ta ruwaito cewa, sunan Oyedepo ya bayyana a cikin takardun Pandora wanda kungiyar 'yan jarida ta International Consortium of Investigative Journalists (ICIJ) suka jagoranta.

Terere: Yadda Fasto Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa
Terere: Yadda Fasto Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Peter Obi, Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da na jihar Osun duk sun bayyana a cikin 'yan siyasan da suka washe kudin kasa suka adana a Turai.

Read also

Jami’an DSS sun kama Hadimin Gwamna, mutum 2 da zargin satar kudin da aka ware wa talakawa

Kamar yadda rahoto ya nuna, Oyedepo a watan Augustan 2007 ya tuntubi Business Centrum Limited, wani agen a London domin su taimaka masa ya kafa kamfani domin kan shi da iyalansa.

"Daga bisani, Business Centrum sun tuntubi Trident Trust Group, daya daga cikin masu boye dukiyoyin sirri kuma sun kasance masu karbar dukiyoyin da aka sato domin adana su.
"An kafa kamfanin Zadok Investments Limited, an kafa shi a ranar 20 ga watan Augustan 2007 da hannun jari 50,000 wanda ko wanne daya ya na da darajar $1.00.
“Duk da Oyedepo da 'ya'yansa maza biyu ne daraktocin kamfanin, sauran iyalansa an bayyana su a matsayin masu hannayen jari.
"Oyedepo da matarsa sun fi kowa yawan hannayen jari inda kowannensu ke da kashi 30, 'ya'yansa maza biyu kowanne ya na da kashi goma yayin da 'ya'ya matan ke da kashi goma kowacce daga ciki

Read also

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

"Takardun ba su bayyana takamaiman kasuwancin da kamfanin ya ke yi ba sai dai hakan ya nuna cewa kamfanin ne iyalan ke adana dukiyoyinsu," rahoton yace.

Tonon asiri: Yadda Stella Oduah ta wawuri N5b, ta siya katafaran gidaje a London

A wani labari na daban, takardun Pandora, daya daga cikin gagarumin binciken watanda da kazaman kudade da aka taba yi a duniya, ya fallasa Sanata Stella Oduah kan yadda a sirrance ta siya katafaren gidaje a London.

Kamar yadda binciken da wata gagarumar kungiyar 'yan jarida ta duniya ya bayyana, sama da 'yan jarida dari shida sun gano cewa wasu manyan gidaje 7 kadarorin Oduah ne da ke London, Daily Trust ta tattaro.

Daya daga cikin kadarorin an siya ne da sunanta, biyu kuwa da sunan kamfanonin Najeriya yayin da hudu daga cikinsu an siya da sunan kamfanin da ke boye mata dukiya na Seychelles.

Read also

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Source: Legit.ng

Online view pixel