Dalla-dalla: Yadda 'yan bindiga suka yi wa jama'a kisan kiyashi a kasuwar Sokoto
- Mazauna yankin kasuwar Goronyo da ke Sokoto sun bayyana yadda 'yan bindiga suka zagaye kasuwar a babura sama da dari
- Sun ce babu shakka shiryayyen farmaki ne da 'yan bindigan na kungiyoyi daban-daban na miyagun suka hada domin tada hankali
- Jama'a da dama sun bayyana cewa 'yan bindigan sun kai farmakin daukar fansa ne kan 'yan sa kai da ke ta kashe Fulani a yankin
Sokoto - Kisan kiyashin da 'yan bindiga suka yi wa jama'a a kasuwar Goronyo da ke gabashin jihar Sokoto a daren Lahadi ya tada hankula.
Ganau sun sanar da Daily Trust a ranar Litinin cewa, mummunan farmakin da aka kai ya kunshi 'yan ta'adda daga mabanbantan kungiyoyi.
Sun ce miyagun sun ajiye banbancinsu tare da hada kai inda suka tsinkayi kasuwar mako-mako ta Goronyo suka dinga harbe-harbe.
Mazauna yankin sun ce kasuwar ta cika dankam yayin da 'yan ta'addan suka bayyana a sama da babura dari kuma suka zagaye wuraren tare da bude wuta kan masu siye da siyarwa, lamarin da ya kawo mutuwar rayuka 49.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Farmakin ranar Lahadin shi ne barnar da ta girgiza karamar hukumar Goronyo, wurin da ya fuskanci hare-hare da suka kai ga rashin rayuka masu yawa, Daily Trust ta wallafa.
Da wannan farmakin Goronyo, sama da rayuka sittin da biyar aka kashe a yankin a cikin kwanaki goma da suka gabata, mazauna yankin suka tabbatar.
A kalla 'yan kasuwa 22 aka halaka a makamancin farmakin da miyagun suka kai kasuwar Unguwan Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar a ranar 8 Oktoba, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da farmakin kasuwar Goronyo a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya a gidan gwamnatin Sokoto.
Ya ce a kalla sama da mutum talatin ne aka tabbatar da mutuwarsu a kasuwar Goronyo duk da har yanzu ana tattaro bayanan.
Farmakin hadin guiwa miyagun suka kai
Kamar yadda lamarin Unguwan Lalle ya faru, wasu mazauna yankin sun alakanta farmakin kasuwar Goronyo da lamurran 'yan sa kai a yankin wadanda suke ta kashe makiyaya domin daukar fansar barnar da ake musu.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce, "Farmakin nan dole a alakanta shi da daukar fansar 'yan sa kai saboda sun kashe makiyaya 11 a kasuwar Mamande da ke karamar hukumar Gwadabawa.
"Kungiyar 'yan sa kan suna ta kamawa tare da kashe Fulani babu gaira, ba dalili," yace.
Wata majiyar wacce ta bada sunanta da Salihu, ta ce maharan sun tsinkayi kasuwar kauyen da dajin Gundumi wanda ke da nisan kilomita kalilan daga kasuwar.
Ragargazar da soji ke yi a Zamfara ne ya tirsasa 'yan bindigan komawa Sokoto, Tambuwal
Gwamna Tambuwal yayin karbar bakuncin Laftanal Janar Yahaya, wanda dan asalin jihar ne, ya nuna damuwarsa kan farmakin Goronyo.
"A safiyar yau mun tashi da mummunan farmaki inda muka rasa rayuka. Har a yanzu muna kirga yawan wadanda muka rasa," yace.
Ya ce hauhawar kashe-kashe a gabashin Sokoto za a iya lakanta shi da yanayin ragargazar da sojoji suke wa 'yan ta'adda a Zamfara.
Asali: Legit.ng