Yan bindiga sun shiga uku: Rukunin karshe na sabbin jiragen yaƙin 'Super Tucano' sun iso Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da isowar rukunin ƙarshe na sabbin jiragen Super Tucano guda 12 daga ƙasar Amurka
- Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace sabbin jiragen 12 sun canza wasan, sojoji na cigaba da samun nasarori
- Ministan ya kuma yi martani kan rahoton cewa rundunar sojojin sama ta biya yan bindiga miliyan N20m don kada su harbo jirgin shugaban ƙasa
Abuja - Gwamnatin tarayya tace rukunin ƙarshe na sabbin jiragen yakin A-29 Super Tucano sun iso Najeriya daga Amurka.
Ministan yaɗa labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, shine ya bayyana haka a wata fira ta wayar salula a shirin "Barka da safiya" na TV Continental, ranar Litinin.
Premium Times ta rahoto cewa ministan ya tabbatar da cewa jiragen da FG ta siya Super Tucano guda 12 daga ƙasar Amurka sun kammala zuwa Najeriya.
Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023
Lai yace:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Gaba ɗaya jiragen Super Tucano guda 12 sun kammala isowa a halin yanzun da nake magana, kuma tuni aka tura su wajen yaƙi a Arewa maso Gabas."
"Kowa na gani sabbin jiragen sun canza wasan, duk wasu nasarori da muka samu kwanan nan saboda sabbin dabaru ne da kayan aiki, ba wai jiragen ne kaɗai ba."
Shin dagaske NAF ta biya yan bindiga miliyan N20m?
Ministan ya kuma bayyana cewa bai ji daɗin labarin da ake yaɗawa ba cewa sojin sama (NAF) sun biya yan bindiga miliyan N20m don kada su kakkabo jirgin shugaban ƙasa.
Daily nigerian ta rahoto ministan yace:
"Sojojin sun musanta rahoton domin zai nuna gazawarsu ne. A tsakanin Zamfara, Katsina da wasu sassan Kaduna da Neja, akwai sansanin yan bindiga 150, shin wanne daga ciki aka baiwa kuɗin?"
"Labarin ma ya saba wa hankali kuma saboda ba su san yadda yan bindigan nan suke bane shiyasa ake yaɗa irin wannan labarin."
A wani labarin na daban kuma Miyagun yan bindiga sun kutsa fadar Basarake, sun yi awon gaba da shi a jihar Katsina
Rahoto ya nuna cewa maharan sun aikata yadda suke so domin katse hanyoyin sadarwa ya shafi garin, babu hanyar neman a kawo ɗauki.
Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, yace hukumar yan sanda bata da masaniya kan faruwan lamarin.
Asali: Legit.ng