Hankula sun tashi, gagararren shugaban 'yan bindiga, Sububu ya koma Sokoto

Hankula sun tashi, gagararren shugaban 'yan bindiga, Sububu ya koma Sokoto

  • Fitinannen dan bindigan Zamfara, Halilu Sububu, ya tattara komatsansa ya koma jihar Sokoto
  • Komawar Sububu Sokoto ta na da alaka da farmakin da sojoji ke kai masa a Shinkafi da ke Zamfara
  • Masana sun ce Sububu ya samu abinda ya ke so tunda Gwalama na da iyaka da Nijar kuma zai iya tserewa can idan an bibiye shi

Sokoto - Bayan watanni kadan da Bello Turji, shugaban 'yan bindiga ya bar sansaninsa da ke Zamfara zuwa Tozai a jihar Sokoto, wani gagararren dan bindiga, Halilu Bello Sububu ya tattara komatsansa tare da komawa dajin Sokoto.

Majiyoyi masu tarin yawa da suka hada da jami'an tsaron sirri, sun bayyana tunaninsu kan dalilin da yasa Sububu ya koma dajin Sokoto duk da sun ce wurin ya mayar sabuwar hedkwatarsa.

Kara karanta wannan

Labarin Abubakar: Matashin Bakano, matukin jirgin sama da ya koma sana'ar dinki

Hankula sun tashi, gagararren shugaban 'yan bindiga, Sububu ya koma Sokoto
Hankula sun tashi, gagararren shugaban 'yan bindiga, Sububu ya koma Sokoto. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Dan ta'addan da ake zargin shi da shirya satar daliban kwalejin koyar da aikin noma da ke Bakura a jihar Zamfara, ya saci sama da mutum tamanin a kauyen Gora da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

An haifi dan ta'addan a garin Sububu da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, Premium Times ta ruwaito.

Sububu ya na daya daga cikin fitattun 'yan bindiga da ake tsoro a jihar kuma an sakankance ya na da alaka da gagararren dillalin makaman nan, Shehu Rekeb.

Sauya wurin zama

Sububu wanda kwamandojinsa ke kira da Halilu Rocket, ya kwashe shekaru a dajin Sububu. Dajin da ke tsakanin Maradun, Shinkafi, Bakura da Talata Mafara a jihar Zamfara da Raba, Tureta, Isa da Goronyo a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

Dukkan majiyoyin da suka zanta da Premium Times sun ce Sububu ya kafa sabon sansaninsa a kauyen Gwalama, kauyen da ke da kusanci da Suruddubu a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Basharu Guyawa, wanda ya ke bibiyar lamurran 'yan bindiga ballantana a Sokoto ta gabas da Zamfara ta arewa, ya ce Sububu ya tsere sakamakon farmakin da jami'an tsaro a Zamfara ke kai masa.

"Na yi imanin cewa dalilinsa na barin Zamfara shi ne farmakin da ake ta kai masa, amma kuma yanzu ya samu abinda ya ke so saboda inda ya koma ya na da iyaka da jamhuriyar Nijar. Zai ya tserewa zuwa Nijar idan ya shiga hatsari," Guyawa yace.

Yadda jami'an tsaro suka yi wa likita da majinyata lugude a asibitin Abuja

A wani labari na daban, an zargi wasu jami'an tsaro da yi wa wata likita da wasu majinyata mugun duka a babban asibitin Maitama da ke Abuja a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun kashe sojoji, sun raunata janar, sun yi awon gaba da motocin soji

Dr. Okpalla Adaeze, daya daga cikin wadanda jami'an tsaron suka nada, ta sanar da Daily Trust cewa wannan cin zarafin aikin wani dan sanda ne da ya zo a duba shi.

Ta ce hakurin sa ya kare ne lokacin da daya daga cikin dakunan suka ki karbarsa, Daily Trust ta ruwaito. Adaeze ta ce ba ta kula shi ba saboda bangaren kula da marasa lafiyan da suka isa asibitin da farko sun kula da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng