EFCC ta yi ram da matashi ɗan Nigeria mai amfani da sunan Mark Zuckerberg wurin damfara a intanet
- Hukumar EFCC ta kama Jatto Sheriff Umar, mai amfani da sunan mai Facebook, Mark Zuckerberg wurin damfara
- Hukumar ta samu nasarar damkar sa da sauran masu shigen laifin sa guda 4 ne a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoban 2021
- Kuma an yanke mu su hukunci daidai da abinda su ka aikata, kotu ta yanke mu su dauri a gidan gyaran hali a Ilorin
Ilorin - Hukumar yaki da rashawa, EFCC, ta kama wani matashi mai shekaru 21, Jatto Sheriff Umar, bayan ya yi amfani da sunan Mark Zuckerberg don damfarar mutane a kafar sada zumunta.
Kamar yadda The Punch ta ruwaito, lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoban 2021, kuma an yanke ma sa hukunci daidai da laifin da ya aikata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hukumar EFCC reshen jihar Ilorin ta tabbatar da yanke wa sauran mutane 4 da aka kama da makamancin laifin sa.
Cikin su akwai Oguntoyinbo Oluwatobi Damilola; Taiwo Akinyemi Kayode daga karamar hukumar Ekiti ta yamma da ke jihar Ekiti, Adebayo Adeola Mark daga Osi, karamar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara, sai Olayinka daga Ilesha da yamma daga jihar Osun tare da wani Yusuf Alameen Abiodun daga yankin Igbo-Owu daga jihar Kwara.
Yayin da aka gabatar da Jatto, Damilola, Taiwo da Mark a gaban alkali Mahmud Abdulgafar na babbar kotun jihar Kwara wacce ke zama a Ilorin, Justice Adenike Akinpelu na kotun ya saurari karar Olayinka da Abiodun.
Duk sun amsa laifukan su
Duk wadanda aka gabatar sun amsa laifukan da ake zargin su da aikata wa.
Innocent Mbachie ne lauyan da ke wakiltar EFCC a gaban alkali Abdulgafar, yayin da R. A Alao ne ya wakilci hukumar a gaban alkali Akinpelu.
Duk lauyoyin biyu sun bukaci kotu ta kula da yadda masu laifukan su ka amsa laifukan su ka yi, da kuma shaidu da aka gabatar gaban kotu kuma a yi gaggawar yanke mu su hukunci.
Alkali Abdulgafar ya yanke wa Jatto hukuncin daurin watanni 6 a gidan gyaran hali na Mandala. Kotu ta bukaci a amshe ma wayar sa kirar iPhone 12 pro, na’ura mai kwakwalwa da kuma takardar fitar da kudi.
Alkalin ya dage daurin Olayinka na watanni 6 kuma ya ci shi tarar N200,000 akan ko wanne laifi cikin laifuka 2 da ya aikata, na damfara da amfani da sunan wani.
Sannan har ila yau, Alkali ya ci Abiodun tarar N200,000. Sannan kotu ta bayar da umarnin amshe wayar sa kirar iPhone XR da yake damfarar da ita.
Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50
Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50
A baya, kun ji cewa Hukumar binciken shari'a na Amurka ya gurfanar da wasu 'yan Nigeria 11 a kotu kan zarginsu da hada baki wurin aikata almundahar kudade, damfara ta banki da satar kudade da sunan wasu.
A ranar Laraba ne Attoni na Kudancin New York, Damian Williams da Jam'in FBI mai kula da New York, Patrick J, Freancy suka sanar da sunayen 'yan Nigeria 11 da ke da hannu wurin karkatar da miliyoyin daloli daga damfarar imel da damfarar soyayya.
Hukumar binciken shari'a na Amurka ta bayyana hakan a ranar Laraba kamar yadda ya zo a ruwayar SaharaReporters.
Asali: Legit.ng