Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona

Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona

  • Yan sanda sun kama wani makiyayi da shanunsa da awaki bayan afkawa gonar wani mutum
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Takatsaba da ke karamar hukumar Suletankarkar a jihar
  • Lawan Shiisu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da afkuwar lamarin

Jigawa - Yan sanda a jihar Jigawa sun kama wani makiyayi mai shekaru 25, wanda aka zargi ya kutsa cikin gonakin wasu ya lalata kayan gona na N200,000 a kauyen Takatsaba da ke karamar hukumar Suletankarkar a jihar.

Jaridar The Guardian ta ruwaito ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da afkuwar lamarin ciin sanarwar da ya fitar a Dutse, ranar Alhamis.

Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona
Taswirar Jihar Jigawa. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

Shiisu ya kuma kara da cewa yan sanda sun kama shanu 73 da awaki 13 da suka kutsa gidan wasu gonaki a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar 2021.

A cewarsa:

"Bayanai da muka samu daga majiya ta bayyana cewa a ranar 10 ga watan Oktoba, misalin karfe 1920hrs, wani makiyayi ya kutsa gonan wani Habu Sa'idu a kauyen Takatsaba da ke karamar hukumar Suletankarkar kuma dabobinsu sun cinye tare da lalata kayan gonar.
"Mazauna kauyen sun ce wasu mutane tare da mai gonar sun tafi domin kallubalantar makiyayin amma ya tada rikici ya yi wa mutane biyar rauni daga cikinsu."

Shiisu ya ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon afkuwar lamarin, yana mai cewa a yanzu komai ya daidaita.

Shiisu ya kara da cewa an fara gudanar da bincike a kan lamarin kuma ana kokarin kamo wadanda ake zargin da aikata laifin.

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164