Rigi Rigi: Muhimman Abubuwan Sani game da Marigayi Sheikh Khalifa Usman Kusfa

Rigi Rigi: Muhimman Abubuwan Sani game da Marigayi Sheikh Khalifa Usman Kusfa

Kaduna - Sheikh Khalifa Usman Kusfa ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malaman addinin Islama dake Jihar Kaduna, wanda ya shafe rayuwarsa wajen koyarwa da kuma wa'azi.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sheikh Usman Kusfa, wanda daukacin al'umma suka sani da sunan "Rigi-Rigi," ya rasu yana da shekara 57 a duniya, bayan ya shafe gomman shekaru yana hidimar addini.

Abubuwan sani game da marigayi Sheikh Khalifa Usman Kusfa, Rigi Rigi
Marigayi Sheikh Khalifa Usman Kusfa (Rigi Rigi) a wajen taron Mauludi. Hoto: Sheikh Usman Rigi Rigi
Source: Facebook

Malamin ya kasance jigo a darikar Tijjaniyya, amma salon wa'azinsa ya ƙetare iyakokin darika, inda ya samu karɓuwa a wajen matasa da tsofaffi saboda sauƙin harshe da barkwanci, in ji wani rahoto na Premier Radio.

Legit Hausa ta rahoto cewa Sheikh Rigi-Rigi ya rasu ne a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairu, 2026, a wani asibiti mai zaman kansa dake Kaduna bayan ya yi fama da jinya na wasu watanni.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Tsohon shugaban babbar jami'a a Arewacin Najeriya ya rasu

Ga wasu abubuwan sani game da Rigi Rigi

1. Asali da kuma zurfin karatun Rigi Rigi

An haifi Sheikh Usman Idris a shekarar 1969 a unguwar Kusfa dake cikin garin Zariya, wani yanki dake alfahari da dadden tushen ilimin addinin Islama da sufanci.

Ya taso ne a cikin gidan ilimi, inda mahaifinsa Sheikh Idris Kusfa ya kafa harsashin karatunsa na farko a cikin zawiyyar gidan wadda ke da babban tasiri.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sheikh Rigi Rigi ya kasance babban masani wanda ya zurfafa bincike a fannoni biyu mafi mahimmanci a ilimin Musulunci, waɗanda sune harsashin gudanar da ibada da kuma fahimtar addini.

  • Ilimin Furu'a (Rassan ilimin Fikihu)

Fannin Furu'a shine ilimin da ya shafi rassan shari'a, watau yadda ɗan adam zai gudanar da ibadunsa na yau da kullum da kuma mu'amaloli.

Sheikh Rigi-Rigi ya shahara wajen bayyana hukunce-hukunce dake kunshe a cikin manyan litattafan fikihu irin su Mukhtasarul Khalil da sauran su.

Kara karanta wannan

Ta fashe: An cafke malaman Musulunci 2 kan zargin jibgar almajiransu har da makami

  • Ilimin Usul (Tushen addini da akida)

Bayan rassan shari'a, Sheikh Rigi-Rigi ya kware a fannin Usul, wanda shine ilimin dake koyar da tushen addini, akida, da kuma yadda ake ciro hukunci daga Alkur'ani da Hadisi.

Wannan haɗaka ta ilimin da na bincike ta ba shi damar duba litattafan magabata da idon basira, yana fitar da bayanan da aka daɗe ba a ji su ba.

Shi ya sa idan yana karatu, yake kawo sunayen malamai irin su Attalili Attagazuti da sauran jiga-jigan malaman tarihi waɗanda ba kowa ne ya san su ba.

2. Shugabanci a zawiyyar Kusfa

Sheikh Rigi-Rigi ya jagoranci Zawiyya Kusfa, wadda matattarar sufanci ce dake ƙarƙashin darikar Tijjaniyya inda ya riƙa koyar da tarbiyya da kuma tsarkake zuciya.

Karatuttukansa sun fi karkata ne kan kyautata dabi'u, daidaita rayuwar zamantakewa, da kuma amfani da Alkur'ani da Hadisi wajen magance dukkan matsalolin yau da kullum.

Ya zama babban jigo wajen shirya taron Maulidi da sauran bukukuwan addini waɗanda suke haɗa kan dubban mabiya daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Da gaske sojojin Amurka sun cafke Sheikh Ahmed Gumi a filin jirgi? Gaskiya ta yi halinta

Salon karatunsa dake ɗauke da sunayen magabata da ambaton Sheikh Ibrahim Niass ya sanya shi zama daban a tsakanin sauran malamai dake birnin na Zariya baki ɗaya.

3. Yadda malam ya samu sunan Rigi-Rigi

Malamin ya shahara wajen lissafa siffofin Annabi (SAW) da na sahabbai cikin gaggawa, wanda hakan ya sa ɗalibansa suka ba shi laƙabin "Rigi-Rigi" saboda yadda kalmomin ke zuba.

Wannan salon ba kawai don nishaɗi ba ne, face hanya ce ta nuna zurfin ilimin da yake da shi a fannin tarihin addinin Islama da sufanci.

A wata hira da jaridar DCL Hausa ta wallafa a shafinta na YouTube, Sheikh Khalifa Usman Kusfa ya bayyana dalilin da ya sa aka sanya masa sunan 'Rigi Rigi.'

Sheikh Rigi Rigi ya ce:

"Game da suna Rigi Rigi, wani lakabi ne da mutane suka sanya mani shi. Rigi Rigi kamar hadari ne, da ya saukar da ruwa mai yawa, irin ruwan dare mai gama duniya, saboda suna samun ilimai masu dimbin yawa daga wajena, shi ne ake ce mun rigi rigi.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An yanke wa tsohon manajan banki hukuncin daurin shekaru 490 a kurkuku

"Ina jin dadi idan aka kira ni da Attalili Attagazuti, saboda sunan waliyyi, ko a kira ni da Rigi Rigi, ko a ce mun Rugum, ko a ce mun Na'Annabi, to wannan na fi jin dadi."

4. Sana'ar Sheikh Rigi Rigi

Baya ga karantarwa da kuma yawon wa'azi, marigayi Sheikh Usman Kusfa ya kasance dan kasuwa, wanda kuma ya kware a sana'o'in hannu.

A hira da aka yi da shi, Sheikh Rigi Rigi ya ce:

"Sana'ata da na taso, na yi dinki ne. Mu a unguwarmu Kusfa, nan cikin Zariya, mun saba da yin sana'o'i, musamman hannu.
"Na yi dinkin keke, na yi na hula, na yi singa, na kuma yi dinkin rigar kaftani, na yi dinkin 'yar Moroko."

5. Alakar Rigi Rigi da Shehu Tijjani

A lokacin da yake raye, Sheikh Rigi Rigi ya bayyana alakarsa da Shehu Tijjani kamar haka:

"Babbar alakata da Shehu Tijjani (R.T.A), na farko shi ne, ni dan darikar Tijjaniyya ne, kuma mahaifina ma dan Tijjaniyya ne, kuma babanshi da kakanshi ma 'yan Tijjaniyya ne.
"Na zo na zama dan Tijjaniyya, watau Murudi kenan na Shehu Tijjani, shi ne shehinmu gaba daya."

Kara karanta wannan

Bayan jiran kusan shekaru 50, Uba Sani ya kaddamar da hanya a kauyukan Kaduna

Abin da matar Sheikh Rigi Rigi ta ce

Yayin da ake zaman makokin malamin, daya daga cikin matan Sheikh Usman Rigi-Rigi Zaria ta bayyana dalilin rasuwar shehin malamin da wasiyyar da ya jima yana nanatawa iyalansa a wata tattaunawa da rediyon RFI Hausa.

Malama Rahmatullahi ta bayyana cewa:

"Shehu ya yi ciwo dai dai gwargwado, ya shekara daya da rabi amma a tsaye yake bai kwanta ba, har sai da Allah ya yi nashi iko, kuma kwanciyarsa gaba daya ba ta wuce kwana biyar ba.
"An kai shi asibitin 44, to a nan ya samu kamar kwanaki 40, kuma a cikin kwanakin ne Allah ya yi masa cikawa.
"Mun yi magana da shi na karshe, muryarsa ba ta canja ba, komai nasa bai canja ba, kamar lafiyarsa kalau. Kullum dai maganarsa, a rike Allah a rike Manzon Allah, a bi shehunnai, a rike zumunci, a rike darikar Tijjaniyya, a hada kan iyali, kullum karatunsa kenan da mu."

Kara karanta wannan

Mutane sun bada mamaki a jana'izar Sheikh Rigi Rigi, an ji sunaye 3 da ake kiransa da su

Malama Rahmatullahi ta ce babban abin da ya fi tsayawa iyalinsa rai shi ne sun so su je su tsaya tare da shi a asibiti, amma ya ce kar su je, su tsaya a gida, wadanda ke tare da shi sun ishe shi.

Matar ta ce sun bi wannan umarni sau da kafa, kuma ba su hadu da shi ba sai da aka dawo masu da gawarsa gida.

Jana'iza da jimamin da aka yi

Dandazon Al'umma sun halarci jana'izar Sheikh Usman Kusfa, Rigi Rigi a Zariya
Daruruwan mutane a wurin jana'izar Sheikh Khalifa Usman Kusfa Hoto: Sheikh Hafram Khaleel
Source: Facebook

An gudanar da sallar jana'izarsa a ranar a cikin birnin Zariya, inda dubban mutane daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan suka hallara domin yi masa ban-kwana.

Legit Hausa ta ruwaito cewa, an gudanar da sallar jana’izar marigayi Sheikh Rigi-Rigi ne a gidansa da ke unguwar Kusfa, cikin birnin Zariya, da yammacin ranar Litinin.

Sallar ta samu halartar manyan malamai, shugabannin al’umma da masoyansa daga ciki da wajen jihar Kaduna. Marigayin ya bar mata hudu, ’ya’ya 37 da jikoki da dama.

An samu rahotanni cewa an kwashe sa'o'i ana gudanar da addu'o'i a makabartar da aka binne shi, yayin da ɗalibansa ke kukan bankwana da malaminsu.

Sheikh Idris Kumbashi Zaria ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, al’ummar Musulmi a Zaria sun rasa babban malami, Sheikh Idris Adam Kumbashi, wanda ya rasu bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan

Zargin lalata da matar aure: Magidanci ya sassara wani mutum da adda har lahira

Sheikh Kumbashi wanda ake kira Abu Sumayya, ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar addini, da'awa da koyarwa lokacin da yake raye.

Al'umma da dama sun yi jimamin rashin malamin addinin wanda suka ce ya yi kaurin suna wurin ilmantarwa da tarbiyyantar da al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com