'Ya Cika Shekara 100,' Tinubu Ya Yabi Dattijon Arewa Tilo da Ya Saura a Tsaransa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Alhaji Tanko Yakasai a matsayin gwarzo daya da ya rage cikin 'yan gwagwarmayar neman ’yancin Najeriya
- Ya ce Tanko Yakasai ya yi rayuwa mai ma’ana tun yana matashi ya ke gwagwarmaya ta hanyar aikin jarida da fafutukar siyasa har ya zama dattijo
- A sakon da ya fitar game da dattijon, shugaba Bola Tinubu ya taya iyalai da abokai murnar cikar Tanko Yakasai shekara 100 a ranar 5, Disamba, 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sakon yabo ga dattijo dan gwagwarmayar ’yancin Najeriya, Alhaji Tanko Yakasai, wanda ya cika shekara 100 a duniya.
A cewar Tinubu, Yakasai shi ne mutum na ƙarshe ya ke raye cikin wadanda suka tsaya tsayin daka wajen neman ’yancin al’umma daga mulkin mallaka.

Source: Facebook
A cikin sakon da hadimin shugaban shugaban ƙasar ya fitar a X, Tinubu ya bayyana Yakasai a matsayin mutum mai jajircewa wanda ya rayu cikin tawali’u kuma ya kafa tarihi mai kyau ta hanyar aiki tukuru da kishin ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dalilin shigar Yakasai gwagwarmaya tun yana matashi shi ne ganin zalunci da cin zarafin da talakawa ke fuskanta a lokacin mulkin mallaka.
Yakasai ya yi kokarin neman ’yanci
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tun yana matashi, Yakasai ya mayar da hankalinsa kan yaki da zalunci a matsayin dan gwagwarmaya, dan jarida da kuma fitaccen mai fafutukar siyasa.
Ya ce shigar sa cikin NEPU, a karkashin jagorancin Malam Aminu Kano, ya zama abin tunawa saboda yadda suka yi gagarumar faɗakarwa a Arewacin Najeriya domin tunkarar mulkin mallaka.
A cewar sakon, wannan fafutuka ta NEPU ta kunna wutar ƙwazo da ƙarfin hali da ta taimaka wajen jan hankalin jama’a zuwa ga neman ’yanci, wanda ya kai ga samun 'yancin kai a shekarar 1960.
Kokarin Tanko Yakasai bayan samun 'yanci
Tinubu ya jaddada cewa bayan ’yancin Najeriya, Yakasai ya ci gaba da nuna cikakken imani ga ci gaban ƙasa ta hanyar rike manyan mukamai.

Source: UGC
Daga cikinsu akwai mukaminsa na kwamishina a Kano a lokacin Audu Bako da kuma matsayin mataimaki na musamman kan alaƙa da majalisar tarayya ga shugaba Shehu Shagari.
Ya ce ko da shekaru sun ja, Yakasai ya ci gaba da zama abin koyi wajen neman haɗin kai, zaman lafiya da ƙarfafar dimokuraɗiyya a Najeriya.
Tinubu ya taya Yakasai murnar cika shekara 100
Shugaban ƙasar ya ce bikin zagayowar shekaru 100 na Tanko Yakasai murna ce ta cika karni guda na hidima ga ’yancin al’umma da dimokuraɗiyya tare da cewa yana taya iyalai, abokai da makusanta murnar wannan rana.
Tinubu ya kammala da cewa yana farin cikin kasancewa cikin masu murnar wannan rana mai muhimmanci ga Alhaji Tanko Yakasai.
Tinubu ya rantsar da ministan tsaro a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya).
Legit Hausa ta gano cewa an rantsar da ministan ne a fadar shugaban kasa da yammacin ranar Alhamis bayan majalisa ta tantance shi.
Janar Christopher Musa ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya a halin yanzu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


