Dangote: Abubuwa 5 game da Mashahurin Attajirin Afrika, yayin da Ya Cika Shekaru 68

Dangote: Abubuwa 5 game da Mashahurin Attajirin Afrika, yayin da Ya Cika Shekaru 68

A ranar 10 ga Afrilu, 2025 ne mashahurin dan kasuwar nan da ya fi kowane dan Afrika arziki, Aliko Dangote ke bikin murnar cika shekaru 68 a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Daga cikin abubuwan da aka san Dangote da su, akwai dade wa yana rike da kambun bakar fatar da ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika.

Aliko
Abubuwan da ya kamata a sani kan Aliko Dangote Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da za su iya jan hankali a kan rayuwar fitaccen dan kasuwar a wannan rahoto;

1. Aliko Dangote bahaushe ne

Alhaji Aliko Dangote ya fito ne daga dangin attajirai ‘yan kasuwa a jihar Kano. Kakansa, Alhassan Abdullahi Dantata, shi ne attajirin da ya fi kowa kuɗi a Yammacin Afirka kafin rasuwarsa a 1955.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Zariya da wani magidanci ya kashe ɗan uwansa da duka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakansa na bangaren uwa, Sanusi Dantata, da kuma ɗan uwansa, Usman Amaka Dantata, sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasuwancinsa.

Mahaifinsa Muhammad Dangote 'dan kasuwa ne kuma 'dan siyasa a yankin Arewa.

2 Yadda Dangote ya samu ilimi

Fitaccen dan kasuwan ya fara karatu a Sheikh Ali Kumasi Madrasa, daga bisani ya tafi makarantar Capital High School a Kano.

Ya samu digiri a fannin nazarin kasuwanci daga jami’ar Al-Azhar da ke Cairo, Masar, daga bisani ya tsunduma harkar kasuwanci yana da shekaru 20.

3. Shugaban rukunin kamfanonin Dangote

PM News ta ruwaito cewa Aliko Dangote ya yi shura a matsayin wanda ya kafa rukunin kamfanonin Dangote a shekarar 1977, a matsayin ƙaramin kamfanin kasuwanci.

Dangote
Wani sashi na matatar Dangote dake Legas Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

A yanzu, rukunin kamfanin ya tumbatsa, inda ake da kamfanoni daban daban da ke sarrafa Sukari, Gishiri, Siminti, Fulawa, Man fetur da sauran nau'ikan kayan amfanin yau da kullum.

3. Dangote: Bakar fata mafi arziki a duniya

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

Mujallar Forbes ta ruwaito cewa Alhaji Aliko Dangote, shi ne attajirin bakar fata mafi arziki a duniya da kimar dukiya da ta kai $23.8 biliyan a watan Maris 2025.

Arzikin 'dan kasuwan ya karu sosai bayan matatar mansa ta fara aiki a Najeriya.

4. Auratayya da iyalan Dangote

Duk da cewa Aliko Dangote bai cika bayyana yadda rayuwarsa ta ke ba, rahotanni sun tabbatar da cewa ya yi auren fari yana da shekaru 20 ga matarsa Zainab, wacce iyaye suka zaba masa.

Allah Ya albarkaci auren da haihuwar ‘ya’ya biyu kafin su rabu. Daga baya ya auri Mariya Muhammad Rufai daga jihar Bauchi, ita kuma sun haifi diya daya kafin su mutuwar auren a 2017.

Rahotonni sun bayyana cewa Dangote na da ‘ya’ya huɗu – ‘yan mata uku da ɗa ɗaya da ya ɗauka, mai suna Abdulrahman.

5. Tasirin Dangote a siyasar Najeriya

Reuters ta wallafa cewa shekarar 2011, tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya naɗa Aliko Dangote a matsayin guda daga cikin 'yan kwamitin kula da tattalin arzikin ƙasa.

Kara karanta wannan

Alkali ya sha da kyar bayan yan ta'adda sun yi ram da shi a Katsina

A shekarar ne kuma ya samu lambar girma ta GCON wanda ake ba mataimakin shugaban kasa.

Dangote ya sauke farashin fetur

A baya, mun wallafa cewa matatar Dangote ta sauke farashin man fetur zuwa N865, bayan gwamnatin tarayya ta amince da yarjejeniyar sayar da mai da Naira.

Rahotanni daga masana’antar mai sun bayyana cewa matatar Dangote ta rage farashin litar man fetur daga N888 zuwa N865, wanda ya wa jama'a daɗi.

Wannan sauyi ya nuna ragin N15 kacal a kowace lita idan aka kwatanta da farashin da ake sayarwa a ranar Laraba, 9 ga watan Afrilu na shekarar 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng