Najeriya Ta Yi Rashi, Attajirin da Ya Kafa Bankin Diamond, Ya Jagoranci MTN Ya Rasu
- Wanda ya kafa tsohon bankin Diamond kuma ya jagoranci kamfanin MTN a Najeriya, Pascal Dozie ya rasu yana da shekaru 85 a duniya
- Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da suka fitar, inda suka ce ya rasu sakamakon rashin lafiya da ke da alaka da tsufa
- An bayyana cewa Dozie ya taka rawa sosai a harkokin kasuwanci da ci gaban bankuna a Najeriya, har ya samu lambar yabo ta kasa ta OON
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fitaccen ɗan kasuwan Najeriya kuma wanda ya kafa Diamond kuma tsohon shugaban kamfanin MTN a Najeriya, Pascal Dozie, ya rasu yana da shekaru 85.
Iyalan marigayin sun fitar da wata sanarwa a ranar Talata, inda suka bayyana cewa ya rasu a ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya da ke da nasaba da tsufa.

Asali: Facebook
Jaridar Business Day ta wallafa cewa dan kasuwar ya bayar da gudumawa sosai wajen cigaban tattalin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasuwar Dozie ta girgiza masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci da bankuna a Najeriya, kasancewarsa cikin 'yan kasuwar da suka kafa tubalin banki mai zaman kansa a ƙasar.
Rayuwa da gudummawar Dozie a Najeriya
Rahotanni sun tabbatar da cewa Pascal Dozie ya kasance mutum mai yawan ilimi a bangaren kasuwanci.
Ya kafa bankin Diamond wanda daga baya aka haɗa shi da bankin Access. Ya kuma shugabanci jami'ar Pan-Atlantic da kamfamin MTN kafin ya sauka daga kujerarsa.
An haifi Dozie a ranar 9 ga Afrilu, 1939 a Egbu, Owerri da ke jihar Imo. Ya karanci tattalin arziki a London School of Economics sannan ya samu digiri na biyu daga City University, London.
Baya ga haka, Dozie ya kafa kamfanin African Development Consulting Group wanda ya yi aiki da manyan kamfanoni irinsu Nestle da Pfizer.
Saboda tarin gudumawar da Pascal Dozie ya bayar, gwamnatin tarayya ta ba shi lambar yabo ta OON.

Asali: Facebook
Iyalai da wasu abubuwa game da Dozie
Marigayi Pascal Dozie ya rasu ya bar mata, Chinyere Dozie da ‘ya’ya guda biyar tare da sauran dangi.
Mutane da dama daga bangarorin rayuwa daban-daban na ci gaba da nuna alhini da kuma tunawa da irin rawar da Dozie ya taka wajen ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba.
Yaushe za a yi jana'izar Pascal Dozie?
Har yanzu iyalansa ba su fitar da jadawalin jana’izarsa ba, sai dai ana sa ran za su sanar da hakan nan ba da jimawa ba.
Yanzu dai kallo ya koma kan iyalan Dozie domin sauraron su saka rana da lokacin da za a yi jana'izarsa.
Malamin Musulunci ya rasu a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Yahya Harun ya kwanta dama.
Sheikh Isa Ali Pantami na cikin malaman Musulunci a Najeriya da suka nuna damuwa kan rasuwar Sheikh Yahya Harun.
Pantami ya bayyana cewa malamin na cikin manyan masu ilimin addini kasancewar yana daya daga cikin wadanda suka yi karatu a jami'ar Musulunci ta Madina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng