Natasha: Akpabio Ya ba da Mamaki da Ya Sumbaci Matarsa a Idon Duniya

Natasha: Akpabio Ya ba da Mamaki da Ya Sumbaci Matarsa a Idon Duniya

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sumbaci matarsa, Ekaette Unoma Akpabio, bayan ta karɓi digirin girmamawa daga Jami’ar Calabar
  • Hakan na zuwa ne yayin da Sanata Natasha Akpoti ke cigaba da jaddada zargin da ta yi wa Akpabio na cewa ya nemi ya yi lalata da ita duk da suna da aure
  • Rahotanni sun nuna cewa, bayan bikin, Akpabio ya wallafa sakon soyayya ga matarsa, ya na yabawa da irin gudunmawar da take bayarwa a rayuwarsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Godswill Akpabio ya ja hankulan jama’a da yadda yake bayyana soyayyarsa ga matarsa a bainar jama’a, lamarin da ke daukar hankalin mutane a shafukan sada zumunta.

A yayin bikin yaye daliban Jami’ar Calabar karo na 37, Akpabio ya sumbaci matarsa, Ekaette Unoma Akpabio, bayan ta karɓi digirin girmamawa.

Kara karanta wannan

Duniyar fina finan Najeriya ta yi rashi, fitacciyar jaruma ta rasu bayan mata tiyata

Akpabio
AkKpabio ya sumbaci matarsa a idon jama'a. Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Bayan taron, Akpabio ya wallafa sakon soyayya ga matarsa a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa, wannan ba shi ne karo na farko da aka ga Akpabio ya na nuna irin wannan soyayya a bainar jama’a ba.

Akpabio ya sumbaci matarsa a bainar jama'a

Bikin yaye daliban Jami’ar Calabar ya gudana ne tsakanin 17 zuwa 23 ga watan Maris 2025, inda aka karrama wasu manyan mutane da digirin girmamawa.

A yayin bikin, bayan da matarsa ta karɓi digirin, Akpabio ya rungume ta sannan ya sumbace ta, lamarin da ya jefa jama’a da dama cikin mamaki da sha’awa.

A hotunan da aka dauka, an ga Akpabio ya na rike da kafadar matarsa, yayin da ita kuma ke riƙe da takardar shaidar digirinta cikin shauki.

Sakon da Akpabio ya tura wa matarsa

Premium Times ta wallafa cewa bayan kammala bikin, Sanata Akpabio ya wallafa wani sakon soyayya mai cike da yabo ga matarsa.

Kara karanta wannan

Barau na kara barazana ga Abba a Kano, 'yan fim din Dadinkowa sun goyi bayansa

Ya rubuta cewa:

“Ga matata, mai girma Ekaette Unoma Akpabio, yayin da ta ƙara samun daraja: ita ce mai ba ni shawara, mai ba ni kwarin gwiwa, kuma cikakkiyar abokiyar rayuwa.”

Ya ci gaba da cewa:

“A yau duniya ta gane abin da ni na sani tun farko, cewa ke mace ce mai muhimmanci, cike da basira da tausayi. Ina taya ki murna da wannan matsayi da kika samu.”
Majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Ra’ayoyin jama’a kan soyayyar Akpabio

Lamarin ya haifar da martani daban-daban daga jama’a a kafafen sada zumunta, inda wasu ke yaba wa Akpabio, wasu kuma na ganin hakan bai dace da mukaminsa ba.

Wasu sun danganta dabi’arsa da irin yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke nuna soyayya ga matarsa a bainar jama’a, musamman lokacin da yake gwamnan Jihar Ribas.

Duk da haka, soyayyar Akpabio ga matarsa na kara jan hankali, inda wasu ke kallon hakan a matsayin abin koyi ga aure mai cike da jituwa.

Kara karanta wannan

An ba kowane sanata $15,000 kafin su amince da dokar ta ɓaci a Ribas? Bayanai sun fito

Aminu Ado ya hadu da Wike a Calabar

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Sarkin Kano na 15 watau Aminu Ado Bayero ya gana da Nyesom Wike a jami'ar Calabar.

Rahotanni sun nuna cewa sun hadu ne a wani bikin yaye dalibai da aka yi kuma aka karrama wasu fitattun mutane a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng