Yadda Jiga Jigan Najeriya Suka Tara Naira Biliyan 17 ga IBB a Zama 1
- Shahararrun attajiran Najeriya sun yi bajakolin gudunmowa a kaddamar da littafin Janar Ibrahim Badamasi Babangida
- A yayin taron, Aliko Dangote ya bada gudunmuwar Naira biliyan 8, yayin da Abdul Samad Rabiu ya bayar da Naira biliyan 5
- Taron da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, yana da nufin tara kudin gina Dakin Karatu na Tsohon Shugaban Kasa, Janar IBB
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An gudanar da gagarumin taro a dakin taro a Abuja, domin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon Shugaban Kasar Mulkin Soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
Littafin mai taken A Journey in Service ya jawo manyan mutane daga sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kasance bako na musamman.

Kara karanta wannan
Atiku, Obasanjo da kusoshin Najeriya sun dura Abuja, IBB zai fitar da babban sirri

Asali: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa taron ya kasance wata dama ta tara kudin gina Dakin Karatu na tsohon Shugaban Kasa IBB, inda manyan attajirai suka bada gudunmuwa mai yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tarawa IBB N17.5bn a Abuja
Shahararren attajirin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya bada gudunmuwar Naira biliyan 8 don tallafawa aikin Dakunan Karatun tsohon Shugaban Kasa IBB.
Aliko Dangote ya kuma bayyana cewa idan aikin ya dauki lokaci fiye da yadda aka tsara, zai ci gaba da bayar da Naira biliyan 2 a duk shekara har sai an kammala shi.
Haka zalika, babban attajirin Najeriya kuma shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya bayar da gudunmuwar Naira biliyan 5.
A yayin taron, wasu fitattun mutane kamar Theophilus Danjuma, ya bayar da gudunmuwar Naira biliyan 3.
The Cable ta rahoto cewa manyan 'yan kasuwa daga ciki da wajen Najeriya sun tara kudi da suka kai N17.5bn domin aikin a cikin 'yan awanni da aka yi yayin taron.

Kara karanta wannan
IBB ya yi fallasa kan zaben 1993 da aka rusa, ya fadi rawar da Buhari ya taka a baya

Asali: Twitter
Dangote ya jinjinawa IBB kan tattali
A cikin jawabinsa, Alhaji Aliko Dangote ya yaba wa Ibrahim Badamasi Babangida bisa sauye-sauyen tattalin arzikin da ya aiwatar a zamanin mulkinsa.
Dangote ya bayyana cewa Babangida ne ya sauya hanyoyin kasuwanci a Najeriya ta hanyar soke tsarin takardun shigo da kaya, wanda hakan ya taimaka wa masana’antu su bunkasa.
Dangote ya ce:
“Saboda irin wadannan sauye-sauye, Najeriya tana da yawan kamfanonin da ke hannun ‘yan kasuwa fiye da kowace kasa a Afrika.”
Ya kara da cewa yanzu haka kaso 85% na tattalin arzikin Najeriya yana hannun ‘yan kasuwa masu zaman kansu, yayin da gwamnati ke da kaso 15% kacal.
IBB ya gina ‘yan kasuwa - Dangote
Aliko Dangote ya bayyana cewa Babangida ne ya kafa tushen kasuwancin ‘yan kasuwa a Najeriya, wanda hakan ya bai wa masu zaman kansu damar habbaka tattalin arziki.

Kara karanta wannan
'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi
Ya ce:
“Yawancinmu da muka samu ci gaba a harkar kasuwanci a yau, mun amfana ne daga irin shirye-shiryen da IBB ya kafa.”
Dangote ya kuma bayyana cewa a da, sai ‘yan kasuwa sun bi ta hannun wasu ‘yan kasuwa daga kasashen waje, musamman Indiyawa, kafin su iya samun lasisin shigo da kaya.
A cewarsa, daga lokacin da IBB ya kawo sauye-sauyen tattalin arziki, an saukaka wa ‘yan kasuwa hanyoyin yin kasuwanci, wanda hakan ya ba su damar bunkasa da habbaka tattalin Najeriya.
Abiola ya lashe zaben 1993 inji IBB
A wani labarin, mun ruwaito muku cewa tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce MKO Abiola ne ya lashe zaben 1993.
Janar IBB ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da littafin da ya rubuta na tarihin rayuwarsa a birnin tarayya, Abuja.
Asali: Legit.ng