Aliko Dangote Ya Fara 2025 da Rashin Sa’a, Ya Sauko a Sahun Attajiran Afrika

Aliko Dangote Ya Fara 2025 da Rashin Sa’a, Ya Sauko a Sahun Attajiran Afrika

  • Ana da labari cewa Aliko Dangote ba shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a yau a cikin kasashen da ke Afrika ba
  • Mai kudin na Najeriya ya rasa kusan Naira biliyan 700, a dalilin haka samu attajirin da ya fi shi arziki a shekarar 2025

Duk yadda Dangote yake ji da dalolin kudi, Johann Rupert shi ne attajirin da bai da sa’a a yau a duk kasashen Afrika

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - A karon farko a sabuwar shekarar nan ta 2025, Aliko Dangote ya yi asara mai yawo da ta jawo ya rasa kambunsa a Afrika.

Kafin yanzu babu mai kudin da ya sha gaban Alhaji Aliko Dangote a duk nahiyar Afrika, hakan ya sa ya zama abin alfahari a duniya.

Aliko Dangote
Akwai wani cikin attajiran Afrika da ya wuce Aliko Dangote kudi Hoto: Getty Imaes
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan da aka samu daga shafin Forbes ya nuna arzikin ‘dan kasuwan ya ragu sosai a ranar Juma’ar da ta wuce, 10 ga Junairu 2025.

Kara karanta wannan

Wani shugaban karamar hukuma ya sake nada hadimai 130 watanni 6 da nadin mutum 100

Mujallar ta ce Aliko Dangote ya rasa $447m ko kuma N693.5bn daga cikin tulin dukiyarsa.

Maganar da ake yi, attajirin ba zai rasa ba Dala biliyan 11.1 baya ba a halin yanzu, sai dai hakan yana nufin an sha gaban shi a Afrika.

Wanene ya zarce Aliko Dangote a Afrika?

Yanzu shugaban kamfanin rukunin na Dangote yana biye da fitaccen ‘dan kasuwan nan, Johann Rupert - mutumin kasar Afrika ta Kudu.

Mista Johann Rupert mai shekara 74 da haihuwa ya mallaki Dala biliyan 11.3 a lissafin karshe da masu bibiyar arzikin suka gudanar.

A fadin duniya, idan ana maganar attajirai, Dangote shi ne na 205 a sahun, sai kuma shi Johann Rupert yake na 200 a halin yanzu.

Ta ina Dangote ya tara makudan kudi?

Dangote mai shekaru 67 shi ne ya mallaki babban matatar mai da ke Legas da mafi girman kamfanin simintin da ake da shi a Afrika.

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Yadda almajiri ya taso ya zama shugaban NNPCL a Najeriya

Mujallar Bloomberg ta ce kafin yanzu arzikin shi ya karu 1% domin tabbatar da matsayinsa.

Bayan harkar gini-gine, a yau Aliko Dangote ya mallaki kamfanonin sukari, gishiri, mai, takin zamani da sauran kayan abinci iri-iri a kasashe.

Asarar da masu kudi suka yi a 2025

Shi kuma Mike Adenuga ya rasa $21m a bana, amma babu mamaki har gobe shi ne na biyu a masu kudin Najeriya, ya mallaki $21m a yau.

Bayan Adenuga akwai Abdulsamad Rabiu wanda rahoton ya ce ya rasa dala miliyan 313 a cikin awanni kusanin 24 da aka rasa kudi.

A Najeriya, Femi Otedola wanda shi ne na hudu ya zama na 2111 a jerin rukunin masu kudin da ake ji da su a duk duniya a shekarar bana.

Dangote ya mallaki sama da N5tr

Kwanaki aka ji labari mai kudin Afrika kaf, mutumin jihar Kano ne, Aliko Dangote wanda dukiyarsa ta fi karfin Naira Tiriliyan 5 a kasuwa.

A jerin namu akwai Sarakai, fitattun ‘yan siyasa da kuma wasu 'ya ‘yan manya, wadanda ba zai yiwu ayi maganar kudi, ba a kira sunayensu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng