'Dan China Ya Yaga Kudin Najeriya a gaban Mahukunta, An Yi Masa Rubdugu a Bidiyo

'Dan China Ya Yaga Kudin Najeriya a gaban Mahukunta, An Yi Masa Rubdugu a Bidiyo

  • Wani dan kasar China ya yayyaga kudin Najeriya a gaban jami'an hukumar LASTMA a jihar Lagos bayan rufe masa kamfani
  • An yada faifan bidiyon dan China inda yake yaga gudan N1,000 cikin fushi wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwa
  • Daga bisani, rundunar yan sanda ta ga faifan bidiyon inda ta bukaci hukumar a jihar Lagos ta fara bincike da daukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Rundunar yan sanda ta ba da umarnin daukar mataki kan wani da ake tunani dan kasar China da ya keta kudin Najeriya.

Kakakin rundunar a Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ya bukaci jami'ansu a jihar Lagos su kaddamar da bincike kan lamarin.

Dan China ya yayyaga kudin Najeriya a Lagos, yan kasar sun kare shi
Rundunar yan sanda ta kaddamar da bincike bayan dan China ya yaga kudin Najeriya a jihar Lagos. Hoto: @dammiedammie35.
Asali: Twitter

Za a binciki dan 'China' da ya yaga kudi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Adejobi ya wallafa a shafin X inda ya bukaci daukar mataki kan haka.

Kara karanta wannan

An soki matar tsohon gwamna da ta kira Najeriya gidan dabbobi, an zagi mijinta a kabari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adejobi ya bukaci kakakin rundunar a Lagos, Benjamin Hundeyin ya tabbatar an fara bincike domin daukar mataki.

Hakan ya biyo bayan wallafa wani faifan bidiyo inda aka ga dan China yana yaga kudin Najeriya a fusace a Lagos.

Wani mai amfani da X, @dammiedammie35 ya wallafa bidiyon inda matashin ya yaga kudin har N1,000 a gaban jami'an hukumar LASTMA.

Jami'an LASTMA sun yi kokarin kama shi

Ana tunanin dan China ya yi haka ne bayan an kulle masa kamfani a kusa da Eko Kate a kan babbar hanyar Lekki zuwa Epe.

Bayan yaga gudan N1,000, jami'an LASTMA sun yi kokarin cafke dan China sai dai wasu yan Najeriya da ake tunanin ma'aikatan kamfanin ne sun kare shi.

Matasan sun yi ta kokarin hana jami'an LASTMA kama dan China inda har suka yi nasarar tseratar da shi, aka boye shi cikin kamfanin.

An yi kaca-kaca da matar tsohon gwamna

Kara karanta wannan

Farfesa Jega ya tona asirin yan Majalisar Tarayya, ya fadi faman da ya yi da su a INEC

Kun ji cewa matar marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta jawowa kanta zagi da kuma mijinta da ke cikin kabari.

Ana zargin Betty Akeredolu ta yi rubutu a shafin X inda ta kira Najeriya da gidan 'zoo' da bai yi wa yan kasar dadi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.