Legas: Ana Fargabar an Damfari Wani Malamin Addinin Musulunci N351,169 a Intanet

Legas: Ana Fargabar an Damfari Wani Malamin Addinin Musulunci N351,169 a Intanet

  • Wani malamin addinin Musulunci a Legas, Abdulrasheed Alaseye, ya fada hannun 'yan damfara' inda ya rasa N351,169
  • Malamin ya biya kudin rajista da sauran kudi domin zama dillalin kamfanin, amma sai suka ci gaba da neman kari
  • Duk da alkawuran dawowa malamin da kudinsa, har yanzu bayan kwana 80, kamfanin ya ki mayarwa malam kudinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Wani malamin addinin Islama a Legas, Abdulrasheed Alaseye, yana neman dauki bayan wani kamfani ya zambace shi N351,169.

Abdulrasheed Alaseye ya bayyana cewa ayyukan kasuwancinsa, ciki har da biyan kudin makaranta na diyarsa, sun tsaya cak saboda da wannan zamba.

Malamin addini ya koka bayan fadawa hannun 'yan damfara'
Legas: Ana zargin wani kamfani ya damfari malamin addinin Musulunci. Hoto: Bill Hinton
Asali: Getty Images

Malami na zargin kamfani da damfara

A zantawarsa da Punch, malamin ya ce ya tuntuɓi Tab Trading Services, wani kamfanin yanar gizo da ke ikirarin ya na dora mutum a kasuwancin layin waya.

Kara karanta wannan

"Ba a fahimce ni ba," Sanata Sani ya faɗi alherin cire tallafin man fetur a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce ya ga tallar kamfanin a shafin X, inda kamfanin ya ce zai horar da mutane yadda za su rika kasuwancin layi da hada katin waya.

A ranar 19 ga Agusta, 2024, Alaseye ya biya N89,919 a matsayin kuɗin farko bayan ya biya kuɗin rajista na N1,950, kamar yadda kamfanin ya bukata.

Yadda kamfanin ya raba malamin da N351,169

Duk da haka, malamin ya ce ya lura kamfanin na ci gaba da neman ƙarin kuɗi. Bayan biyan N351,169, Alaseye ya nemi a mayar masa da kuɗinsa amma hakan ya ci tura.

Da malamin ya matsa a kan a mayar masa da kudinsa, kamfanin ya yi alkawari zai mayar da kudin amma sai bayan kwanaki 29, kuma zai cire wani kaso.

Bayan kusan kwanaki 80, ba a mayar masa da kuɗin ba, malamin ya sake kara matsawa kamfanin, inda aka ce masa rashin lafiyar ma’aikaci ne dalilin jinkirin.

Kara karanta wannan

Tsadar fetur: Mazauna Kano sun hakura da hawa mota, sun nemawa kansu mafita

Kamfanin ya karya alkawarin tura kudi

A ranar 25 ga Oktoba, 2024, Ken, wani daraktan Tab Trading Services, ya tabbatar wa jaridar cewa za su biya malamin kuɗinsa kafin ranar 30 ga Oktoba, 2024.

Ken ya bayyana cewa aikin kamfanin shine koyar da dillacin layukan waya. Ya ce jinkirin biyan ya faruwa ne saboda ƙarin kuɗin da suka yiwa malamin na N53,000 da bai biya ba.

Da ranar ta zo, Tab Trading Services ya turawa malamin N1,999 kacal, kuma har zuwa lokacin wallafa wannan labari, kamfanin bai karasa cika kudin ba.

'Yan damfara sun yiwa banki kutse

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake zargin 'yan damfara ne sun yi kutse a yanar gizon bankin Guarantee Trust a Najeriya.

Bankin ya fitar da sanarwar kan labarin cewa yan damfara sun yi kutse tare da niyyar kwashe bayanan abokan hulda, amma hakan bai yiwu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.