Lagbaja: Muhimman Abubuwa 5 a kan Shugaban Sojojin Najeriya da Ya Rasu

Lagbaja: Muhimman Abubuwa 5 a kan Shugaban Sojojin Najeriya da Ya Rasu

  • A yau Talata fadar shugaban kasa ta tabbatar da rasuwar shugaban sojojin kasan Najeriya Laftanal Janar Taoreed Lagbaja
  • Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya rasu bayan wata jinya mai tsanani da ya yi duk da cewa ba a bayyana menene yake damunsa ba
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani a kan tsohon shugaban sojin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sanarwar rasuwar hafsun sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja.

An ruwaito cewa Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya rasu ne bayan wata jinya mai tsanani da ya yi fama da ita.

Kara karanta wannan

Ana jimamin mutuwar Janar Lagbaja, tsohon hafsan tsaro ya yi babban rashi

Taoreed Lagbaja
Abubuwa 5 kan marigayi Laftanal Janar Taoreed Lagbaja. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Legit ta haɗa muku rahoto a kan wasu muhimman abubuwa 5 da suka shafi Laftanal Janar Taoreed Lagbaja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Wurin haihuwa

An haifi Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne a karamar hukumar Irepodun ta jihar Osun duk da cewa ya shafe kuruciyarsa a Osogbo.

Haka zalika an tabbatar da cewa an haifi Laftanal Janar Taoreed Lagbaja a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 1968.

2. Shiga aikin soja

Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya shiga makarantar sojoji ta NDA a shekarar 1987 kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Bayan kammala digirin farko a NDA, marigayin ya tafi Amurka karin ilimi inda ya samo digiri na biyu.

3. Jgorantar yaki

Marigayi Laftanal Janar Lagbaja ya jagoranci yakin mai suna Operation Harmony IV a yankin Bakassi.

Haka zalika ya jagoranci runduna a kasar Congo karkashin majalisar dinkin duniya da kuma Operation Zaki.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Hafsan sojojin kasan Najeriya ya rasu, Tinubu ya fitar da jawabin gaggawa

4. Zama shugaban soji

Shugaba Bola Tinubu ya nada Laftanal Janar Taoreed Lagbaja matsayin shugaban sojin kasan Najeriya a ranar 19 ga watan Yunin 2023.

Marigayin ya rike matsayin har lokacin da rai ya yi halinsa a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamban 2024.

5. Mata da 'ya'ya

Jaridar the Nation ta wallafa cewa Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya rasu yana da mata daya a duniya mai suna Mariya.

A karshe, marigayin ya rasu ya bar ya'ya biyu a duniya kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

An karawa Olufemi Oluyede matsayi

A wani rahoton, kun ji cewa mukaddashin hafsan sojojin Najeriya, Olufemi Oluyede ya samu karin girma zuwa matsayin Laftanar Janar a soja.

Kafin karin girman, Oluyede yana rike da matsayin Manjo Janar ne lokacin da aka naɗa shi mukaddashin hafsan sojojin kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng