An Ba Babban Malamin Izala Darika yayin Ziyarar Shehi, Jama'a Sun Tayar da Kura

An Ba Babban Malamin Izala Darika yayin Ziyarar Shehi, Jama'a Sun Tayar da Kura

  • Al'umma sun fara ce-ce-ku-ce bayan Sheikh Abubakar Salihu Zariya ya kai ziyara ga babban malamin darikar Tijjaniyya
  • Yan Izala da dama sun soki malamin kan ganin bai kyauta ba a matsayinsa na babban malami kuma ya ziyarci Shehin Darikar
  • Sai dai Sheikh Abubakar Salihu Zariya ya bayyana dalilin da ya sanya shi kai ziyara ga babban malamin darikar Tijjaniyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Hira ta zama sabuwa bayan babban malamin Izala, Sheikh Abubakar Salihu Zariya ya ziyarci malamin Darika, Sheikh Usman Rigi Rigi a Zariya.

Yan Izala da dama suna ganin cewa bai kamata Sheikh Abubakar Salihu ya kai ziyara ga malamin Darikar ba saboda irin maganganun da yake.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya ji korafe korafen yan Najeriya, ya sallami Ministoci 5

Sheikh Attalili
Alkali Salihu Zariya ya ziyarci Malam Attalili. Hoto: Abubakar Salihu Zariya
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Yasir Haruna Muhammad ya wallafa a Facebook, Sheikh Abubakar Salihu ya bayyana dalilin kai ziyarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar Salihu Zariya ya ziyarci Shehin Darika

Sheikh Abubakar Salihu ya kai ziyara ga malamin Darika, Sheikh Usman Rigi Rigi da aka fi sani da Sheikh Attalili Attaguzuti.

Sheikh Usman ya shahara da ambaton tarihi da sahabban Gausun Darika, Sheikh Ahmadu Tijjan da mutane suke ganin ba su kama hankali ba.

Hakan ya saka yan Izala da dama, ciki har da Sheikh Ibrahim Disina yin martani a Facebook ga Sheikh Salihu Zariya.

Dalilin kai ziyarar Sheikh Salihu Zariya

Sheikh Abubakar Salihu Zariya ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne domin ya tabbatar da abin da malamin Darikar ke fadi.

A karkashin haka Sheikh Abubakar Salihu ya ce sun dauki lokaci suna tattaunawa musamman kan abubuwan da yake fada da ake ganin sun saɓa hankali.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi barazanar sauke sarakuna saboda rashin tsaro

An ba malamin Izala Darika yayin ziyara

A lokacin da malaman suka hadu, cikin raha Sheikh Usman Riji Riji ya ce ya ba Sheikh Abubakar Salihu Zariya darika.

Haka zalika Sheikh Abubakar Salihu Zariya ya ce ya ba babban malamin Darikar Tijjaniyyar Izala.

Shugaban Izala ya rasu a Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa an sanar da cewa Allah ya yi wa shugaban Izala na jihar Kebbi rasuwa bayan jinya a jihar Sokoto.

Al'ummar Musulmi a fadin Najeriya sun tura sakon ta'aziyya ga kungiyar Izala da iyalan malamin bisa rashin da suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng