Malamin Addinin Ya Fadi yadda Ya Zama Dan Fashi da Makami a Shekarun Baya

Malamin Addinin Ya Fadi yadda Ya Zama Dan Fashi da Makami a Shekarun Baya

  • Wani malamin addinin Kirista da ya fi shahara da suna Ndabosky ya tayar da kura a kafafen sadarwa bayan wani bayani da ya yi
  • Fasto Ndabosky ya bayyana cewa ya taba zama ɗan ta'adda wanda ya yi fashi da makami a shekarun baya saboda wajen da ya girma
  • Haka zalika faston ta bayyana yadda cikin taimakon Ubangiji mahaifiyarsa ta ceto rayuwarsa daga fashi da makami zuwa fasto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Wani fitaccen malamin addinin Kirista a birnin Onitsha ya fadi tarihin yadda ya yi fashi da makami.

Fasto Chukwuemeka Ohanaemere da aka fi sani da Ndabosky ya ce ya shiga fashi da makami tun yana dan karami.

Kara karanta wannan

Bayan cire VAT a gas da dizil, gwamnati ta yi albishirin saukin farashin wutar lantarki

Nnabodosky
Fasto ya fadi yadda ya taba zama dan fashi. Hoto:@Baldilocks
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa faston ya ce an haife shi a wani waje mai mugun haɗari ne a birnin Onitsha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin addini ya yi fashi da makami

Fasto Chukwuemeka Ohanaemere ya ce ya taba zaman dan fashi da makami lokacin yana dan shekaru 14 da haihuwa.

Faston ya bayyana cewa ya yi ta'addanci sosai a wancan lokacin kafin Ubangiji ya ceto rayuwarsa ya koma hidimar addini.

Chukwuemeka Ohanaemere ya bayyana cewa ya girma ne a yankin Nnewi a Onitsha wanda waje ne mai hadari kuma hakan ne ya yi tasiri a rayuwarsa.

Yadda Ubangiji ya ceto malami daga fashi

The Guardian ta wallafa cewa Fasto Chukwuemeka ya ce Mahallicinsa ya yi amfani da mahaifiyarsa wajen ceto rayuwarsa daga fashi da makami.

Ndabosky ya ce a baya ya zama mai barazana ga rayuwar al'umma amma cikin ikon Allah yanzu ya zama mai ba su kariya.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

A kwanakin baya faston ya yi zazzafan gargaɗi ga masu sukansa inda ya ce zai yi maganinsu da kansa.

An kama yan fashi da makami a Jigawa

A wani rahoton kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya a jihar Jigawa ta yi nasara kan wasu yan fashi da makami da suka addabi al'umma.

Cikin miyagun da rundunar ta kama, har da babban ɗan fashi da makami da ya fitini mutane a Jigawa da wasu sassan Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng