Wani Ɗan Najeriya Ya Saki Matarsa Makonni Kadan da Yin Aurensu, Ya Bayyana Dalili
- Wani dan Najeriya ya shiga shafukan sada zumunta inda ya bayyana yadda ya rabu da matarsa makonni kadan da yin aurensu
- Cike da bakin ciki mutumin ya ba da labarin abin da ya faru har ta kai ga ya rabu da matar tasa duk da basu gama cin amarci ba
- A zantawarmu da Dakta Shamsu Abubakar, ya ce gwajin kwayoyin sikila na da fa'ida tun kafin soyayyar saurayi da budurwa ta kai ga maganar aure
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wani dan Najeriya mai suna Maya Santos, ya girgiza mutane bayan da ya sanar da cewa ya rabu da amaryarsa kasa da wata biyu da aurensu.
Mista Maya Santos ya wallafa hotonsa tare da matarsa a shafukan sada zumunta lamarin da ya karo jawo ce-ce-ku-ce ganin soyayyar da ke a fuskokinsu.
Dan Najeriya ya rabu da amaryarsa
Matashin ya ba da labarin mutuwar auren nasa ne a shafinsa na TikTok, @mayasantos636 .
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
@mayasantos636 ya bayyana cewa sun yi aure ne a ranar 5 ga Mayu, 2024, kuma sun rabu ne a watan Yuli saboda matsalar kwayoyin halitta (genotype a turance).
Yayin da yake bayyana bakin cikinsa kan rabuwarsu, mutumin ya ce ya zama dole su sawwakewa juna tun yanzu domin gujewa wahalar da za su shiga a gaba.
Matsalar kwayar halitta ta raba aure
Ya yi addu'a ga matar da suka rabu yana mai cewa:
"Mun yi aure a ranar 5 ga Mayun 2024. Mun rabu a cikin watan Yuli 2024 saboda matsalar kwayoyin halitta.
"Ubangiji ya sani ina matukar sonki amma dole mu rabu domin samawa kanmu sauki da kuma gudun shiga garari na har abada.
"Ina addu'a Ubangiji ya kawo maki madadina a cikin kankanin lokaci. Za ki ci gaba da kasancewa a cikin zuciyata har Abada. Ina kewarki."
Gwajin kwayar halitta na da fa'ida
A zantawarmu da Dakta Shamsu Abubakar, wani likita daga jihar Katsina, ya ce kuskure ne saura da budurwa su nutsa a soyayya har ta kai ga maganar aure ba tare da sun yi gwajin kwayoyin halitta ba.
Dakta Shamsu ya ce idan aka samu saurayi da budurwa na dauke da kwayar sikila, to likita kan ba su shawarwari na illolin da ke tattare da hakan a kimiyance.
Likitan ya ce idan mace da namiji na dauke da kwayar sikila (AS, AS) to akwai yiwuwar su haifi yaro mai sikila a mizanin 1 bisa 4 (kashi 25).
Ya ce akwai yiwuwar a samu yaro wanda shi kuma yana dauke da kwayar sikilar ne, a mizanin 2 bisa 4 (kashi 50) da kuma yiwuwar a haifi yaro marar sikila ko kwayar sikilar a mizanin 1 bisa 4 (kashi 25).
Da wannan ne Dakta Shamsu ya ke ganin gwajin kwayoyin halitta na da muhimmanci domin gujewa hayayyafar yara masu sikila wanda dawainiya da su kan iya jigatar da iyaye.
Sadaja ta sa miji ya saki matarsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani magidanci ya saki matarsa da ke kwance a gadon asibiti a Kano saboda ta karbi sadakar N100,000 amma ta ki ba shi komai.
An ce wasu ne suka shiga asibitin suna rabawa marasa lafiya sadakar kudi inda rabo ya rantse da matar. Sai dai mijin ya nemi a bashi N50,000 a ciki, ita kuma matar ta hana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng