Fitacciyar Mawakiyar Musulunci a Najeriya, Rukayat Gawat Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Fitacciyar Mawakiyar Musulunci a Najeriya, Rukayat Gawat Ta Rigamu Gidan Gaskiya

  • Mun samu labarin rasuwar shahararriyar mawakiyar Musulunci a Najeriya, Rukayat Gawat, lamarin da ya jefa masoyanta cikin alhini
  • Da sanyin safiyar ranar Talata, 24 ga Satumba, 2024, aka fitar da labarin mutuwar tauraruwar mawakiyar a dandalin sada zumunta
  • Masoyan marigayia Rukayat da dama sun shiga yanar gizo suna alhinin rasuwarta yayin da suke nuna matukar abin da ya kai ga rasuwarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Rahotanni sun bayyana cewa shahararriyar mawakiyar addinin Musulunci Rukayat Gawat Oyefeso ta rasu, lamarin da ya jefa masoyanta cikin alhini.

A ranar 24 ga Satumba, 2024, malamin addinin Islama na Ilorin, Alfa Aribidesi At-Tawdeeh ya sanar da labarin rasuwar mawakiyar.

Kara karanta wannan

Mutuwar Sanata ta dakatar da zaman majalisar tarayya, bayanai sun fito

Allah ya karbi rayuwar mawakiyar Musulunci, Rukayat Gawat
Allah ya yiwa mawakiyar Musulunci, Rukayat Gawat rasuwa. Hoto: @iamrukayatgawat
Asali: Instagram

Mawakiyar Musulunci ta rasu

Alfa Aribidesi At-Tawdeeh ya wallafa a shafinsa na Facebook tare da hoton marigayiyar yana mai nuna alhinin rasuwarta da kuma yi mata addu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar malamin:

“Muna mika sakon ta'aziyyarmu ga iyalan Ruqayat Gawat bisa wannan babban rashi! Allah ya gafarta mata kurakuranta! Ruqayat Gawat ta rasu."

Duba sanarwar da ya fitar a kasa:

Rukayat dai ta shahara a rera wakokin addini wanda hakan ya sa ta samu dimbin masoya a tsakanin al'ummar Musulmi.

Kawo yanzu dai ba a san cikakken bayani game da rasuwar ta ba amma dai masoyanta sun nuna matukar alhinin mutuwarta.

Masoyan Rukayat Gawat sun yi alhini

Ba da jimawa ba labarin rasuwar Rukayat Gawat ya bazu a shafukan sada zumunta, kuma magoya bayansa sun yi ta ta’aziyya.

Itz Holarjumoke:

"Allah ya sanya ta a mafificin gida a Al Jannah."

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su wataya: Tinubu ya sanya ranar fara biyan sabon albashin N70000

Hajia Anunimorigba Onaopemipo:

"Allah ya gafarta mata kurakuranta, kuma ya sanya ta a Aljanatul Firdausi."

Onikoko Kudirat:

"Subuhanallahi. Allah ya karbi ibadunta ya shigar da ita cikin Aljannah da rahamarsa".

Ayodeji Tanwa:

"Allah ya jikanta da rahma, ya gafarta mata kurakuranta, ya sanya Aljanah Firdausi ta zamo gidanta na karshe."

Orunsolu Jelilat Abdulazeez:

"Subhanallah, Allah Ta'ala ya gafarta mata zunubanta, kuma ya sanya mata matsayi mafi girma a cikin Aljannah".

Mawakiyar yabo ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa an shiga jimami bayan samun labarin rasuwar fitacciyar mawakiyar yabo na addinin Kirista, Aduke Ajayi da aka fi sani da Aduke Gold.

An ruwaito cewa mawakiya Aduke Gold wadda ta ba da gagarumar gudunmowa a wakokin yabon addinin Kirista ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.