Babban Malamin Musulunci Ya Rasu a Arewacin Najeriya

Babban Malamin Musulunci Ya Rasu a Arewacin Najeriya

  • A ranar Alhamis aka wayi gari da rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Zakariyya Adam Alhassan Jos
  • Malam Zakariyya Adam Alhassan ya kasance daya daga cikin malamai da suke da ƙoƙari wajen shiga ƙauyuka domin isar da sako
  • Malaman addini daga jihohi da dama sun fara isar da sakon ta'aziyyar rasuwar Sheikh Zakariyya ga iyalansa da al'ummar Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Al'ummar Musulmi a Arewacin Najeriya sun yi rashin babban Malamin addini, Sheikh Zakariyya Adam Alhassan Jos.

Sheikh Zakariyya Adam Alhassan Jos ya rasu ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba a jihar Filato.

Sheikh Zakariyya
Malamin addini ya rasu a Filato. Hoto: Abu Fauzan
Asali: Facebook

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya wallafa sakon ta'aziyyar rasuwar malamin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Ahmad Isa: Mai gabatar da shirin Rai Dangin Goro a gidajen rediyo ya kwanta dama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rasuwar Malam Zakariyya Adam Alhassan

A yammacin jiya Alhamis iyalan Sheikh Zakariyya Adam Alhassan Jos suka sanar da rasuwarsa a jihar Filato.

Wasu daga cikin daliban malamin sun bayyana cewa ya yi jinya a kwanakin baya duk da ya sanar da su cewa ya samu sauki.

A yau Jumua'a ne za a yi sallar gawar Sheikh Zakariyya a birnin Jos kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Ayyukan addini da Sheikh Zakariyya ya yi

Sheikh Zakariyya Adam ya kasance malami ne da ke shiga ƙauyukan Fulani domin wa'azi a Arewa ta Tsakiya da Arewa Maso Gabas.

Haka zalika yana karantar da al'umma a wurare daban daban a jihar Filato inda suka hada da Dogon Ƙarfe, Bukuru da Low Cost.

Malamai sun yi ta'aziyyar Sheikh Zakariyya

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi na cikin waɗanda suka nuna alhini kan rasuwar Malam Zakariyya Adam Alhassan Jos.

Kara karanta wannan

Yadda mutuwar dan ta'adda Halilu Sububu za ta takaita ayyukan ta'addanci a Arewa

A wani bangaren, Sheikh Musa Yusuf ya wallafa sakon jaje da addu'ar Allah ya gafarta wa Malam Zakariyya a shafinsa na Facebook.

An kashe malamin addini a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa wani matashi ya hallaka mahaifinsa wanda babban Fasto ne mai suna Isaac Umurie yana tsaka da bacci a jihar Delta.

An tabbatar da cewa matashin mai suna Ufuoma Umurie yana hannun ƴan sanda wanda aka tabbatar yana fama da ciwon tabin hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng