Soshiyal Midiya: Cristiano Ronaldo Ya Kafa Tarihi, Ya Zarce Kowa Yawan Mabiya a Duniya

Soshiyal Midiya: Cristiano Ronaldo Ya Kafa Tarihi, Ya Zarce Kowa Yawan Mabiya a Duniya

  • Fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya sake kafa wani sabon tarihin na tara mabiyan da suka haura biliyan daya
  • An rahoto cewa Cristiano Ronaldo ya tara wadannan mabiyan ne daga shafukan Instagram, Facebook, Twitter, YouTube da sauransu
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan ya kafa tarihin cin kwallaye 900 a Portugal da duka kungiyoyin da ya bugawa wasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwanaki kadan bayan da ya kafa tarihi na cin kwallaye 900, Cristiano Ronaldo ya sake kafa wani sabon tarihin na tara mabiyan da suka haura biliyan daya.

A kaf masu amfani da soshiyal midiya a duniya, babu wanda ya kai Cristiano Ronaldo yawan mabiya a shafukan Instagram, Twitter, Facebook da sauransu.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki Musulmi ya zabgawa malamin addini mari a bidiyo, ya fadi dalili

Cristiano Ronaldo ya godewa masoyansa yayin da ya tara mabiya biliyan 1 a soshiyal midiya
Cristiano Ronaldo ya tara mabiya biliyan 1 a shafukan sada zumunta. Hoto: @Cristiano
Asali: Twitter

Mabiyan Cristiano Ronaldo sun kai biliyan 1

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, Cristiano Ronaldo ya ce lallai a yanzu ya kafa tarihi, kuma hakan ta faru sakamakon aiki tukuru.

"Mun kafa tarihi, mabiyana sun kai biliyan 1! Wannan ya wuce a kira su da tarin lambobi kawai, shaida ce ga sha'awarmu, jajurcewarmu, da kuma ƙauna ga wasan."
Tun daga titunan Madeira zuwa manyan filayen wasanni a duniya, koyaushe ina taka leda ne domin dangina da ku, kuma yanzu biliyan 1 daga cikinmu suna tare da ni."

- A cewar Ronaldo.

Ronaldo ya godewa mabiyansa

Fitaccen dan wasan na Portugal kuma mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr, ya ce mabiyansa sun kasance tare da shi duk rintsi duk wuya.

Kara karanta wannan

Soshiyal Midiya: Jaruman Kannywood 10 da suka fi yawan mabiya a Facebook, Instagram

Cristiano Ronaldo ya ce:

"Wannan nasarar ta mu ce baki daya, kuma a tare ne muka nunawa duniya cewa ba mu da wani sha-maki kan abin da za mu iya cimmawa.
"Na gode da yakininku a kaina, da goyon bayan da kuka ba ni, da kuma kasancewa wani bangare na rayuwata."

Ya kuma tabbatarwa mabiyansa cewa har yanzu akwai sauran nasarori a gaba kuma a tare za su sake kafa wani tarihinin bayan cimma nasarori masu yawa.

Mabiyan Ronaldo a soshiyal midiya

  • Facebook - 170.5m
  • Instagram - 639m
  • Twitter - 113m
  • YouTube - 60.6m
  • Kuaishou - 9.4m
  • Weibo - 7.5m

Cristiano ya shirya yin ritaya?

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya yi bayani kan shirinsa na yin ritaya daga buga kwallon kafa.

Cristiano Ronaldo ya ce ba zai fadawa kowa ba idan lokacin ritayarsa ya yi, sai dai kuma ba zai karbi aikin horar da 'yan wasa ba idan ya daina taka leda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.