Kwalliya Ta Zo da Gardama: Budurwa Ta Sheka Lahira a Wajen Tiyatar Karin Mazaunai
- Wata matashiya ta mutu a dakin tiyata yayin da aka je yi mata karin mazaunai ta hanyar dabarar 'BBL' a yankin Lekki a jihar Legas
- Rundunar 'yan sandan Legas, wadda ta tabbatar da mutuwar matashiyar ta ce sun kama ma'aikaciyar jinyar da ta gudanar da aikin
- Masana sun yi gargadin cewa matsalolin da ke biyo baya ko ke faruwa lokacin tiyatar BBL ta karin duwawu na iya kai ga ajali
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - An shiga tashin hankali a yankin Lekki da ke Legas bayan da wata matashiya da aka bayyana da Abiola ta mutu yayin da ake yi mata tiyatar karin mazaunai.
An ce yanzu haka jami’an ‘yan sandan Legas sun kama wata ma’aikaciyar jinya bisa mutuwar Abiola mai shekaru 36 a yankin na Lekki da ke jihar.
Jaridar The Nation ta bayar da rahoton cewa matashiyar ta rasu ne bayan da aka yi mata aikin kara girman mazaunai a wani asibiti da ke Lekki-Phase 1.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalubalen tiyatar karin mazaunai
Shugaban kungiyar likitocin tiyatar sauya kamanni ta Amurka (ASPS), Dakta J. Peter Rubin ya ce ana yin tiyata 'BBL' ne domin kara girman duwawu ta hanyar cire kitse daga wasu sassan jiki.
Kamar yadda rahoton Plasticsurgery.org ya nuna, adadin wadanda suka mutu daga tiyatar BBL ya kai daya cikin 3,000, wanda ke nuna karuwar yawan mace-macen.
Duk da irin nasararin da ake samu na tiyatar karin mazaunai sakamakon amfani da dabarun tiyata na zamani, an ruwaito Dakta Rubin na cewa:
"Ya kamata masu son karin mazaunai su sani cewa wannan tiyatar ta na da hatsari, wanda kan iya kai ga mutuwa."
Matashiya ta mutu a dakin tiyata
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da mutuwar matashiyar a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce direban matashiyar ne ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sanda na Maroko.
"Jami'an 'yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, sun tattara hujjoji, sun duba tare da daukar hoton gawar matar, sannan suka kai gawar dakin ajiye gawa domin yin bincike.
"An kama ma'aikaciyar jinyar da ta yi aikin yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin."
- A cewar sanarwar Benjamin.
An fasa aure saboda mazaunai
A wani labarin mun ruwaito cewa wani ango ya ce ya fasa auren masoyiyarsa da suka shafe dogon lokaci suna soyayya saboda ya gano tana amfani da mazaunan roba.
Fitacciyar mai ayyukan jin kai, Fauziyya D. Sulaiman ta yi kira ga 'yan mata da su gyara halayensu musamman a kan yin ciko a mazaunai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng