Kwalliya ta zo da gardama bayan da ciwo ya kama wata budurwa da aka karawa mazaunai a Najeriya
- Wata 'yar kwalisa a Najeriya taje anyi mata tiyatar kara girman mazaunai
- Tiyatar ta lakume mata Naira miliyan 3
- Yanzu haka dai tace kugun ta da baya na mata ciwo sosai
Fitattar 'yar kwalisa a Najeriya mai suna Precious Chidinma Ogbulu ta yi bayani bayan da tayi tiyatar karin mazaunai a 'yan watannin da suka gabata bayan ta biya zunzurutun kudi har Naira miliyan 3.
KU KARANTA: Saadiyya Gyale ta karyata labarin mutuwar ta
Sai dai Precious dake karin bayani ta bayyana cewa har yanzu bayan ta da kugu suna yi mata ciwo tun bayan da akayi mata tiyatar domin ta kara kyau a idon duniya.
Legit.ng dai ta samu cewa mata da yawa kan shiga halin kaka-nika-yi musamman saboda ganin sun burge al'umma ko kuma maza inda sukan jefa rayuwar su cikin matsala babba.
Sai dai kuma ita Precious din tace taji dadi da aka yi mata tiyatar domin yanzu zata kara kyau kuma surar ta za ta fito sosai ba kamar da ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng