"Da Hankalina," Matar da Ta Kekketa Fasfon Mijinta a Filin Jirgi Ta Fadi Dalilin Hakan

"Da Hankalina," Matar da Ta Kekketa Fasfon Mijinta a Filin Jirgi Ta Fadi Dalilin Hakan

  • Wata mata mai suna Ella Jeffery ta yi bayanin abin da ya tunzura ta har ta kai ga yayyaga fasfon mai gidanta lokacin da su ka iso Najeriya
  • Wannan al'amari ya dauki hankali matuka, har ta kai ga hukumar shige da fice ta kasa ta fara bincike a kan lamarin da ya auku a bainar jama'a
  • Sai dai Ella Jeffery ta bayyana cewa kamata ya yi a ji ta bakinta, domin haka kawai ba za ta yaga fasfon mijinta ba sai da wani dalili

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - Wata mata mai suna Ella Jeffery ta dauki hankulan masu amfani da shafukan sada zumunta da hukumar shige da fice da ta kasa bayan yaga fasfon mijinta.

Kara karanta wannan

Direban adaidaita sahu ya maida jakar kudin da ya tsinta, yan sanda sun sa cigiya

Lamarin ya yadu, wanda ya sa wasu ke zaton ko Misis Ella na da tabin hankali, kuma hukumar shige da fice ta fara bincike, amma ta ce ya kamata a ji ta bakinta.

Jejoja Family TV
Matar da ta yaga fasfon mai gidanta ta yi bayanin dalilinta Hoto: Jejoja Family TV
Asali: Facebook

A bidiyon da ta wallafa a shafinsu na Facebook, matar ta bayyana cewa ta na sane da duk abin da ta aikata, kuma ta yi haka ne saboda ta gaji da wulakancin mai gidanta da danginsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Miji na ya takura mani," Ella

Matar nan da ta yi daidai da fasfon mai gidanta a filin jirgin Legas, Ella Jefferey ta bayyana cewa mai gidanta da 'yan uwansa sun dade su na tauye hakkinta.

The Nation ta wallafa cewa duk da matar ba ta bayyana hakikanin abin da ake yi mata ba, amma ta zargi mahaifiyarsa da yan uwansa da juya akalar gidanta.

Kara karanta wannan

"Duk arzikinmu?" Kashim Shettima ya ga rashin dacewar fama da talauci a Arewa

"Ni ba mahakaciya ba ce. Na dade ina jure abubuwa da yawa, har yanzu mahaifiyarsa da yayarsa ke juya shi."
"Na yi abin da na yi. Babu wanda zai kama ni. Na sha wahala da shi" inji Ella.

An kama wata da zargin kashe mijinta

A baya mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta damke wata mata, Rahimat Salaum da ake zargi da kashe mai gidanta, Shehu Salaum.

'Yan sandan sun cafke Rahimat bayan ta na kokarin guduwa da kayan marigayin mijin, kuma ta jagoranci jam'an tsaron har wurin da gawar Salaum ke kwance.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.