An Ga Bidiyo Ta Koma Talla, Jama'a Sun Kawowa Tsohuwar Malamar Makaranta Tallafi

An Ga Bidiyo Ta Koma Talla, Jama'a Sun Kawowa Tsohuwar Malamar Makaranta Tallafi

  • Wata tsohuwar malamar makarantar Liberty a Ikota da ke jihar Legas, za ta samu tallafin kudi bayan an gano bidiyon yadda ta koma talla
  • A lokacin zanga-zangar adawa da manufofin Bola Tinubu, an gano tsohuwar malamar, Folake Olaleye ta na kukan yadda yunwa ta addabe ta
  • 'Yan Najeriya sun bazama titunan kasar nan domin gudanar da zanga-zangar neman sauyi a manufofin gwamnati da ya jawo matsin rayuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - Hankalin mahukuntan makarantar Liberty da ke Ikota a jihar Legas da masu amfani da shafukan zumunta ya kai kan tsohuwar malamar makarantar, Folake Olaleye.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnatin Kano ta ɗauki matakai 6, ta yi magana kan ɗaga tutar Rasha

An gano Misis Folake ta na talla yayin zanga-zanga, tare da kukan cewa yunwa ta addabeta, kuma ba ta da yadda za ta ciyar da yaranta.

Legas
Za a tallafawa tsohuwar malamar makaranta a Legas Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa makarantar Liberty ta sallami tsohuwar malamar daga aiki a shekarar 2020 bayan mahukuntan makarantar sun ce ta fadi jarrabawar tantance malamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yunwa za ta kashe ni,' Misis Folake

Wannan tsohuwar malamar makaranta a jihar Legas ta bayyana cewa da kyar ta ke iya ciyar da kanta da yaranta abinci sau daya a rana.

Folake Olaleya ta bayyana cewa yunwa za ta yi masu illa, kuma da kyar ta ke ci gaba da gudanar da rayuwar yau da gobe, Premium Times ta wallafa.

"Wannan gwamnati za ta kashemu ne? Tunani zai kashe ni. Ba zan iya kai ga ci gaba da rayuwa ba. Abin ya yi yawa. Ya kamata gwamnati ta kawo mana dauki," inji ta.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Bayan rasa rayuka, masu zanga zanga sun fara alkunutu a Kano

Makarantar Liberty za ta taimaki Folake

Mahukuntan makarantar Liberty sun bayyana cewa za a taimakawa tsohuwar malamarsu.

Makarantar ta ce an kori malamar bisa ka'ida, kuma yaranta na ci gaba da karatu kyauta a makarantar kafin ta cire su domin radin kanta.

Matasa sun janye zanga-zangar yunwa

A wani labarin kun ji cewa wasu matasa masu gudanar da zanga-zanga sun bayyana janyewa daga fita domin nuna fushinsu daga rashin saukin rayuwa.

Daya daga cikin jagororin zanga-zangar a Legas, Hassan Taiwo Soweto ya bayyana cewa ba za su ji fargabar wata barazana da hukumomin tsaro za su yi masu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.