"Yadda Na Haifi Yara 100 a Kasashe 12 Duk da Ban Taba Yin Aure ba," Shugaban Telegram
- Shugaban kamfanin Telegram, Pavel Durov ya shaidawa duniya cewa a yanzu haka yana da 'ya'ya 100 a sassa daban daban na duniya
- Abin da ya fi ba kowa mamaki game da wannan magana shi ce, Mista Durov bai taba yin aure ba har kawo yanzu da ya kai shekara 39
- A cewar mamallakin Telegram ya sami yaran ne ta hanyar ba da sadakar maniyyinsa ga iyalan da ba sa iya daukar ciki da kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wanda ya kirkiri dandalin Telegram, Pavel Durov ya fallasa wani sirri mai ban mamaki game da haihuwar yara 100 da ya ce ya yi duk da bai taba yin aure ba.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram din a ranar Litinin da yamma, dan kasuwan mai shekaru 39 ya ba da labarin yadda ya kai ga haihuwar ‘ya’ya da dama.
Durov ya ba da sadakar maniyyinsa
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kimanin shekaru 15 da suka gabata ne wani abokin Mista Durov ya tuntube shi a kan ya ba da gudunmawar maniyyinsa a asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce matar abokin ce ta gaza daukar ciki saboda wata matsala, inda suka nemi Mista Durov da ya ba da gudummawar maniyyinsa domin matar ta dauki ciki.
Da farko Mista Durov ya ce yana da shakku, amma daraktan asibitin ya shawo kan shi, wanda ya bayyana maniyyinsa a matsayin "mai inganci" da cewar yin hakan aikin jama'a ne.
Shugaban Telegaram na da 'ya'ya 100
Mista Durov ya bayyana cewa:
“Ba a jima da fada mani cewa cewa ina da yara sama da 100 ba, wadanda na haifa ta dalilin ba da gudunmawar maniyyina ga ma'auratan da suke gaza daukar ciki da kansu."
Ya bayyana cewa gudummawar maniyyinsa da ya bayar ya taimaka wa ma'aurata 100 a cikin ƙasashe 12 domin ba su damar rainon ciki da kuma goyonsa, inji rahoton The Cable.
Duk da cewa ya dauki shekaru bai ba da gudummawar ba, ya bayyana cewa har yanzu asibitin IVF yana da ragowar daskararren maniyyinsa domin amfani ga iyalai masu neman haihuwa.
'Yar shekara 70 ta haifi tagwaye
A wani labarin, mun ruwaito cewa asibitin karbar haihuwa da kula da mata na kasa-da-kasa da ke Uganda ya sanar da cewa dattijuwa 'yar shekaru 70 ta haihu a asibitin.
A cewar asibitin a shafinsa na Facebook sun yi amfani da fasahar IVF akan dattijuwar, lamarin da ya sa ta shiga tarihi na zama mace ta farko da ta haihu bayan ta kai shekara 70 a Afrika.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng