Al’ajabi: Rafin da Mutane Masu Neman Haihuwa da Waraka Ke Zuwa Addu’a

Al’ajabi: Rafin da Mutane Masu Neman Haihuwa da Waraka Ke Zuwa Addu’a

  • A wani abun al'ajabi da Legit.ng ta samo daga jihar Ondo, an samu wani rafin da ake zuwa addu'a a cikinsa
  • An bayyana cewa, rafin ya kasance wajen da mata masu neman haihuwa ke zuwa domin addu'ar neman haihuwa
  • A cewarsa dan jagoran da ya kai wakilin Legit.ng rafin, mata da yawa sun samu biyan bukata a rafin na Arun

An gano wani rafi da mutane masu neman haihuwa da waraka daga cututtuka daban-daban ke zuwa domin addu'a a wani yankin jihar Ondo.

A wata ziyara zuwa tsaunin Idanre da ke a jihar Ondo, tawagar Legit.ng ta gano wani rafi mai ban al'ajabi wanda aka yi ikirarin yana warkar da dukkanin cututtuka, kuma yana magance matsalar rashin haihuwa ga mata.

A cewar Mista Paul, dan jagoran ziyarar, mata da yawa sun bayar da shaida tare da tabbaci na abubuwan al'ajabin rafin inda suka dauki ciki kuma suka haifi yara bayan shan ruwan rafin.#

KARANTA WANNAN: Wata Kungiyar Igbo Ta Bayyana Farin Ciki da Kame Nnamdi Kanu, Ta Bayyana Dalili

Al'ajabi: Rafin da mutane masu neman haihuwa da waraka ke zuwa addu’a
Tsaunukan Idanre a jihar Ondoake, inda rafin Arun yake | Hoto: wikipedia.org
Asali: UGC

Wakilin Legit.ng, yayin da yake tattaunawa da jagoran, ya yi masa tambayoyi domin samun cikakken bayani game da rafin da ake kira Arun, da kuma yadda ake amfani da ruwansa wajen addu'ar neman haihuwar da ma ta waraka.

A cewar dan jagoran:

"A yayin da kake sha, ko yin wanka a cikin ruwan, ka tabbatar da cewa ka yi addu'a akan dukkanin matsalar dake damunka, saboda ruwan yana magance kowace irin matsala.
"Arun, wani rafi ne wanda ke magance matsaloli da yawa, kuma muna samun tabbaci daga mutanen da suka yi amfani da ruwan wannan rafin.
"Akwai wata mata da tazo ta debi ruwan rafin, ta yi amfani dashi, kuma ta haifi jaririnta.

Wannan rafi mai matukar ban mamaki da al'ajabi ya kasance a saman wani tsauni mai tsawo sama taku 3,000.

Wani karin abun al'ajabin dake tattare da ruwan rafin shine, mutune kan iya deban ruwansa su tafi dashi gida domin amfani dashi, amma dole su hada da dutsen cikin rafin saboda ya kiyaye dandano da kuma kasancewarsa ruwan rafin.

KARANTA WANNAN: 'Yar Shugaba Buhari Ta Ciri Tuta, Ta Yi Digirgir a Daukar Hoto a Kasar Waje

Da aka tambayi Mista Paul game da deban ruwan ba tare da dutsen cikin rafin ba, ya amsa da cewa:

"Da zaran ka sanya dutsen rafin Arun a cikin ruwan da ka deba, to dandanonsa zai ci gaba da kasancewa na rafin Arun. Amma matukar baka sanya dutsen ba, dandanon zai sauya, zai zama ba dadi.

Kalli cikakken bidiyon ziyarar da Legit.ng ta kai zuwa rafin Arun.

'Yan Sanda Sun Shiga Shagali Bayan Da ’Yar Sanda Ta Haifi Jarirai ’Yan Uku

A wani labarin daban, Wata ‘yar sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun, Bolaji Senjirin ta haifi 'yan uku - maza biyu da mace daya, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Edward Ajogun, ya ziyarci dangin a yankin Kemta na garin Abeokuta a ranar Laraba tare da mambobin kwamitin hulda da jama'a na 'yan sanda (PCRC).

Ajogun ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa yadda ya ba su kyautar jariran lafiya, yana mai bai wa dangin tabbacin ci gaba da ba su kulawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel