Telegram ta yi fintinkau yayin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki

Telegram ta yi fintinkau yayin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki

  • Manhajar Telegram ta yi fintinkau yayin da mahajojin Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki
  • Wannan na zuwa ne a yau Litinin kwatsam kawai aka ga manhajojin sun tsaya da aiki cak
  • Kamfanin Facebook ne mai mallakar Instagram da WhatsApp, manhajojin da ke gaba a fannin sadarwa

Tsarin dandamali aike sakon nan take na yanar gizo, Telegram, ya maye gurbin Facebook cikin sauri har ma da dandamali WhatsApp da Messenger, bayan da aka samu barakar da ta sa manhajojin suka daina aiki.

Kamar Facebook da dandamali masu alaka da shi, Telegram ma na ba da damar kiran bidiyo, VoIP, tura fayil da sauran fasali da yawa, Leadership ta ruwaito.

An kaddamar da mahajar a kan tirken iOS a ranar 14 ga Agusta, 2013 da kuma Android a watan Oktoba 2013.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Telegram ta yi fintinkau yayin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki
Manhajar Telegram | Hoto: callbell.eu
Asali: UGC

A baya mun kawo muku rahoton cewa, kamfanin Facebook wanda shi ne mamallakin WhatsApp, Instagram da Messenger ya samu matsalar da masu hulda dashi suka koka rashin aikinsa a yau Litinin 4 ga watan Oktoba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu amfani da manhajojin sun koka kan cewa, ba sa iya amfani dasu wajen tura sakonni ko karba, inji rahoton Independent.

Kamfanin mai kimar dala tiriliyan, wanda ke alfahari da masu amfani da aiki dashi da suka kai biliyan 2.9 a kowane wata, ya kasance a kasa akalla sa'o'i biyu kenan.

A lokaci guda, hannun jarin Facebook ya sauka kusan da kashi 5.5%.

Wannan ya biyo bayan hauhawar farashin hannun jari na baya-bayan nan yayin da Facebook ke fuskantar bincike a Majalisar Dattawan Amurka bayan da wani mai tonon asiri, Frances Haugen, ya fallasa wasu takardun cikin gida ga Jaridar Wall Street.

Kara karanta wannan

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

Yadda kotu ta daure wani mutum shekaru 10 kan satar da abokinsa ya tafka

Wani matashi a kasar Ghana da aka fi sani da Kofi Sarfo ya ba da labarin wani abin bakin ciki da ya faru dashi kuma ya tilasta masa yin shekaru 10 masu kyau na rayuwarsa a gidan yari.

A cikin hirar da yayi da gidan talabijin na SV TV Africa, mutumin ya bayyana cewa yana can yana zaune lafiya wata rana abokinsa ya kawo kudi GHc3,600 (N244,442.97) don ya ajiye a dakinsa saboda suke kashewa kadan-kadan har su kare.

Kofi bai sani ba cewa an sato kudin ne daga hannun wani mutum, kuma tuni da ma ya dukufa don nemo wadanda suka masa barnar domin ya kamo su ya mika ga doka ta yi aikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel