Gwamna Ya Fadi Abin da Ya Faru Bayan Sun Fadi Gaskiya Ga Janar Babangida a Mulkin Soja

Gwamna Ya Fadi Abin da Ya Faru Bayan Sun Fadi Gaskiya Ga Janar Babangida a Mulkin Soja

  • Tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba ya bayyana yadda suka yi alaka da Janar Ibrahim Badamasi Babangida
  • Mista Olusegun Osoba ya yi ikirarin cewa Ibrahim Badamasi Babangida ya fada musu wanda suka juya mulkinsa
  • Tsohon gwamnan ya bayar da labarin ne kasancewar a lokacin mulkin sojan Janar Babangida yana aikin jarida

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Tsohon gwamna jihar Ogun, Olusegun Osoba ya tuna baya kan yadda Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi mulkin soja.

Olusegun Osoba ya bayyana cewa ya yi mu'amala da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne a matsayinsa na dan jarida a shekarar 1985.

Kara karanta wannan

Jigon APC a Arewa na yi wa Tinubu maƙarƙashiya? Gaskiya ta bayyana

Janar IBB
Yadda mulkin Janar Babangida ya kasance. Hoto: Francois-Xavier Harispe
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Olusegun Osoba ya bayar da labarin ne bayan ya samu ganawa da tsohon shugaban sojan a lokacin da yake kan karaga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe IBB ya yi juyin mulki?

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi juyin mulki ga Janar Muhammadu Buhari ne a shekarar 1985.

Cikin manyan dakarun Najeriya da suka taimakawa Janar Babangida wajen juyin mulkin akwai Janar Sani Abacha, Aliyu Gusau da sauransu.

Osoba: 'Mun fadi gaskiya ga IBB'

Olusegun Osoba ya ce a matsayinsa na dan jarida ya bayyanawa Janar Babangida abubuwan da yake yi da ba su dace ba.

Osoba ya ce sun fadawa Janar Babangida gaskiya ne wata rana shi da Felix Peter da wasu yan jarida guda daya ko biyu, rahoton the Cable.

IBB: 'Ni ma ɗan amshin shata ne'

A cewar Olusegun Osoba, a lokacin da suka fadi gaskiya ga IBB sai yace musu shi ma ba shi yake juya mulkinsa ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya mayar da martani bayan harbin Donald Trump, ya yi gargadi

Janar IBB ya fada musu cewa, a cewar Osoba, sojoji da suka taimaka masa ne suke juya mulkin kuma idan ya saba musu za su tumbuke shi.

Yaron IBB ya yi hadarin mota

A wani rahoton, kun ji cewa Mohammed Babangida, yaron tsohon Shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota.

Mummunan al’amarin da ya lakume rayukan akalla jami'an tsaro uku wadanda ke cikin ayarin Mohammed Ibrahim Babangida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng