Shin ko kun san wakar da duk wanda ya kunna ta za’a ci tararsa Naira 100,000?
- Hukumar dake kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa ta dauki tsattsauran mataki kan wakar mawaki Falz
- A sanarwar da hukumar ta fitar duk Radiyon da ta sake ta kunna wakar za'a ci tarar ta
- Wannan mataki ya biyo bayan wasu kalamai na batanci da wakar take kunshe da su
An haramta kunna wakar da wani mawaki mai suna Falz yayi mai taken This is Nigeria a duk gidajen Radiyon dake fadin kasar nan.
Hukumar dake kula da kafafen sadarwa ta kasa (NBC) ceta sannar da hakan a cikin wata zungureriyar wasikar sanarwa da ta fitar wadda aka aikewa da gidajen Radiyon.
Koda a kwanakin baya sai da kungiyar kare musulmai ta kasa (MURIC) ta yi yunkurin shigar da mawakin kara kafin daga bisani ta canza shawara ta fasa kais hi kotun.
KU KARANTA: Kwastam tayi babbar nasarar damke maganin Kodin, tsala-tsalan motoci da wasu mutane 8
Duk gidan radiyon da yayi kasassabar kunanna wakar zai biya Naira 100,000 lakadan.
Tun da farko dai hukumar ta NBC ta bayyana wakar a matsayin wacce take cike da zambo da kuma zagi ga al'ummar kasar nan. musamman a cikin wani baiti da ya ke alamta al'ummar kasar nan a matsayin masu aikata laifi.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng