Mun fasa kai karar Falz akan wakar Shaku Shaku – Kungiyar kare hakkin Musulmi

Mun fasa kai karar Falz akan wakar Shaku Shaku – Kungiyar kare hakkin Musulmi

Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC tace ta fasa daukar mataki akan faifan bidiyon mawaki Falz wanda ya haddasa cece-kuce.

Ta bayyana kudirinta na janye kai karan a ranar Litinin, 11 ga watan Yuni.

A wata sanarwa da kungiyar Musulunci ta saki tace “sakamakon ban hakuri da ta samu daga manyan masu fada a ji na kasar,” ta yanke shawarar kai mawaki ga hukumomin tantance fina-finai na gwamnati.

Ta ce wannan yunkuri zai zamo izina ba wai ga Falz kadai ba harma ga sauran mawaka.

Mun fasa kai karar Falz akan wakar Shaku Shaku – Kungiyar kare hakkin Musulmi
Mun fasa kai karar Falz akan wakar Shaku Shaku – Kungiyar kare hakkin Musulmi

Kungiyar tace wakar na iya jnyo rikicin addini dama na kabilanci idan akayi sakaci.

KU KARANTA KUMA: 2019: Talakawa ne zasu yanke hukunci kan wanda zai zamo shugaban kasar Najeriya na gaba - Keyamo

Idan baza ku manta ba a makon da ya gabata ne kungiyar MURIC ta ba mawakin wa’adin kwanaki bakwai ya janye bidiyon daga kasuwa ko ya ga sammaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel