“Tapswap Ya Daina Aiki”: Budurwa Ta Yi Bayani Game da Mining Ɗin da Ƴan Najeriya Ke Yi

“Tapswap Ya Daina Aiki”: Budurwa Ta Yi Bayani Game da Mining Ɗin da Ƴan Najeriya Ke Yi

  • Wata budurwa ta ce babu bukatar daga hankali idan Tapswap ya ki budewa a halin yanzu, tana mai lura da cewa matsala ce ta bai daya
  • Ta na magana ne kan korafe-korafen mutanen da ke hakar hakar ma'adinan Tapswap a halin yanzu da ke fatan za su fitar da kudi na gaba
  • A zantawar Legit Hausa da Jibrin Y Lanval, ya ce mutane ne suka yi wa Tapswap yawa a halin yanzu, shi ya sa ya ke ba da matsala

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wata budurwa da ke harkar hakar ma'adanan Tapswap ta kwantar da hankulan wadanda ke fuskantar matsala a yayin shiga manhajar a yau Alhamis.

Mutane da dama sun yi korafi kan yadda ba sa iya bude manhajar Tapswap a wayoyinsu, abin da ya jefa su a fargaba ganin ba a taba samun irin wannan matsalar ba.

Kara karanta wannan

Notcoin vs TapSwap: Abubuwa 5 game da tara kudin Crypto ta hanyar dangwale a Telegram

Budurwa ta yi bayani kan dalilin kin budewar manhajar Tapswap
Mutane na korafin ba sa iya buɗe Tapswap ɗin su. Hoto: Photo credit: TikTok/Ose Sweet and Getty Images/Xavier Lorenzo.
Asali: Getty Images

Ma'abota amfani da TikTok sun ce manhajar Tapswap ba ta buɗewa, amma matar ta ba su tabbacin cewa matsala ce da kowa ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Tapswap ba ya budewa?

A cikin wani bidiyon TikTok, Ose Sweet ta ce ita ma ta sami irin wannan matsalar a lokacin da ta ke ƙoƙarin buɗe Tapswap.

An tabbatar da bayanin matashiyar Ose game da Tapswap a cikin wata sanarwa daga dandalin manhajar Tapswap na Telegram, inda aka ce ana kokarin gyara matsalar.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Zuwa ga masoyan Tapswap, a halin yanzu muna kan yin gyara. Wannan gyaran na iya ɗaukar tsakanin sa'a ɗaya zuwa uku. Mun gode da haƙurin ku."

Mutane sun yiwa Tapswap yawa - Jibrin

Wani Jibrin Y Lanval da muka zanta da shi kan wannan matsalar, ya ce mutane ne suka yi wa Tapswap yawa a halin yanzu, shi ya sa ya ke ba da matsala wajen shiga.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya fadi ainihin lokacin da ya fara mulkin jihar Rivers

Jibrin Lanval ya tuna cewa an taba samun irin wannan matsalar a wasu 'minings' din da aka yi a baya kuma daga baya duka aka gya matsalar.

A yayin da ya ke kara wa matasa kwarin guiwar daukar 'magirbi, diga da cebura' domin hako ma'adan crypto, Jibrin ya kuma gargade su a kan saka kudi a cikin harkar ba tare da ilimi ba.

"Mining Halal ne" - Farfesa Yelwa

Tun da fari, mun ruwaito cewa wani babban malamin addini, Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ba da fatawa a kan mining inda ya bayyana cewa ya hallata a shiga

Farfesa Mansur ya fara da cewa idan har ma'anar mining shi ne wani ya sa ayi masa aiki, misali wannan da mutane ke tara lambobi domin ya biya su, to mining ya halatta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.