“Ta Yi Dacen Dangi”: Bidoyon Alatun da Wata Amarya Ta Samu Ranar Aurenta Ya Jawo Magana

“Ta Yi Dacen Dangi”: Bidoyon Alatun da Wata Amarya Ta Samu Ranar Aurenta Ya Jawo Magana

  • Wani mutum ya jawo cece-kuce a yanar gizo yayin da yake baje kolin kyaututtukan kayan alatu daban-daban da dangi suka baiwa wata amarya
  • Mutumin ya kasance a wurin daurin auren amaryar kuma ya dauki lokacinsa wajen nadar bidiyon kayan alatun da amaryar ta samu
  • A cewar mutumin, abin da dangin amaryar suka aikata ya kasance al’adar mutanen unguwar Umuezukwu ne da ke Onicha Igboeze a jihar Ebonyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Domin nuna mata gata yayin da za a kai ta dakin aurenta, dangin amarya sun hada kayan alatu daban-daban da za su 'yarsu gidan miji da su.

Mutane sun magantu kan kayan alatun da wata amarya ta samu
Dangi sun hadawa wata amarya kayan alatu masu yawa a ranar aurenta na gargajiya. Hoto: @lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

An hadawa amarya kayan alatu

Wani mutum wanda ya dauki hoton bidiyon kayayyakin, ya ce al’adarsu ce a unguwar Umuezukwu, jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Yaki da garkuwa da mutane: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 85 da ake zargin 'yan ta'adda ne

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

@lindaikejiblogofficial ya wallafa bidiyon mutumin da ke nuna kyaututtukan da aka shirya a wurin daurin auren na gargajiya.

Kyaututtukan sun haɗa da tukunyar gas, gado da katifa, tukwane, teburin cin abinci da sauransu.

Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu kan wadannan kayan alatu:

Kalli bidiyon kayayyakin a nan kasa:

Abin da mutane ke cewa:

maxhubonline ya ce:

"Wannan al'ada ce, ta yi dacen dangi, kamar yadda wata mata da 'yan uwanta suka ba ta kyautar mota, kowane iyali na yin hakan gwargwadon karfinsu."

ahseeaa ya ce:

"Wannan tsohuwar al'ada ce a Arewa, amarya ta zo da gadaje da sauran kayan daki har da ma garar abinci, shi kuma ango ya kai mata kayan lefe ya tanadi gidan da za su zauna."

uchescouc ya ce:

"Abin da ya saba faruwa ne wannan a karamar hukumar Njidaka ta jihar Anambra, Idu ulo, mutumin da ya wallafa wannan bidiyo ya yi kauyanci, kamar bai taba ganin irin haka ba."

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da aka kashe a harin Kogi ya karu, an roki Tinubu ya dauki mataki

Landan zuwa Legas: Nubi ta iso Nijeriya

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa Pelumi Nubi, matashiyar da ta tuka mota daga Landan zuwa Legas ta iso Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa Nubi ta fuskanci kalubale a kan hanyarta, ciki har da hatsarin mota, amma a karshe ta cimma muradinta

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.