Jerin Manyan Mata 10 Mafi Arziki a Duniya da Adadin Kudin da Suka Mallaka
A wannan shekarar ta 2024, akalla 369 cikin 2,781 mafi arziki a duniya mata ne, kenan suna da kaso 13.3% na jerin, kuma yawansu ya karu ne daga 337 da aka samu a 2023.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Tattalin arzikin mata ya fara samun gurbin zama a mujallar Forbes, wacce ke fitar da jaddawalin mutane mafi arziki a duniya.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Mace mafi arziki a duniya da ke rike da kambun a shekaru hudu a jere, a cewar Forbes, ita ce Françoise Bettencourt Meyers, an ce ta samu ribar da ta haura dala biliyan 19 a 2024.
Jerin mata 10 mafi arziki a duniya
Mata tara daga cikin 10 mafi arziki a duniya sun gaji dukiyarsu daga ubanninsu, mazaje ko kuma uwa (a mafi karancin lokuta).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mujallar Forbes ta bayyana cewa ta tattara bayanan dukiyar matan ne ya zuwa ranar 8 ga watan Maris, 2024.
10. Abigail Johnson
Abigail Johnson, wacce 'yar kasar Amurka ce ta mallaki dukiyar da ta kai $29bn, kuma tana da shekaru 62 a duniya.
An ruwaito cewa ta samu arzikinta daga hannun jarin kamfanin Fidelity Investment, kuma ita ce ta 10 a jerin mata mafi arziki a duniya.
9. Gina Rinehart
Gina Rinehart ta mallaki dukiyar da ta kai darajar $20.8bn a yayin da take da shekaru 70, kuma 'yar kasar Austaraliya ce.
An ruwaito cewa ta mallaki dukiyar ta ne daga hakar ma'adanai da noma. Ita ce mace ta 9 a jerin mata mafi arziki a duniya.
8. Miriam Adelson da zuriyarta
Miriam Adelson da zuriyarta sun mallaki dukiyar da ta kai darajar $32bn, tana da shekaru 78 a yanzu, kuma 'yar kasar Amurka ce.
An ruwaito cewa Adelson da zuriyarta ne mamallakan babban gidan caca na Las Vegas Sands, kuma ita ce ta 8 a jerin mata mafi arziki a duniya.
7. Rafaela Aponte-Diamant
Ita kuwa Rafaela Aponte-Diamant, ta kasance 'yar kasar Switzerland da Italiya, kuma arzikinta ya kai $33.1bn yayin da take da shekaru 79.
Aponte-Diamant da mijinta Gianluigi Aponte sun kafa wani kamfanin safarar kaya ta hanyar ruwa a 1970, kuma ita ce ta bakwai a jerin mata mafi arziki a duniya.
6. Savitri Jindal da zuriyarta
Savitri Jindal da zuriyarta sun mallaki dukiyar da ta kai $33.5bn, a yanzu da take da shekaru 74 a duniya, tana rayuwa ne a kasar Indiya.
An ce Jindal ce mace mafi arziki a Indiya, kuma ta shida a mata mafi arziki a duniya, tana da kamfanin tama da karafa wanda ya shahara a duniya.
5. Mackenzie Scott
A 2019 ne Mackenzie Scott ta datse aurenta da mijinta Jeff Bezos, inda ta samu kudin saki na kaso 4% na kadarar kamfanin Amazon.
A yanzu darajar dukiyarta ta kai $35.6bn a yayin da take da shekaru 53, kuma tana zaune a kasar Amurka a matsayin mace ta biyar a jerin mafi arziki a duniya.
4. Jacqueline Mars
Magajiyar kamfanin The Mars Inc. ta kasance mace ta hudu a jerin mata mafi arziki a duniya. A yanzu tana da shekaru 84 a duniya.
An ruwaito cewa Mars ta mallaki dukiyar da ta kai $38.5bn daga wannan kamfani, kuma tana zama a kasar Amurka tare da kannenta.
3. Julia Koch da zuriyarta
Julia Koch ta mallaki dukiyar da ta kai $64.3bn a shekaru 61, ita da 'yayanta uku na da kaso 42% na hannun jarin kamfanin Koch wanda ke harkar mai da kayan kiwon lafiya.
Koch ta kasance 'yar kasar Amurka, kuma ta zama ta uku a mata mafi arziki a duniya, bayan ƙaruwar arzikinta a 2024.
2. Alice Walton
Ita kuwa Alice Walton, mai shekaru 74 a duniya, ta kasance 'yar kasar Amurka, kuma mace ta biyu a mata mafi arziki a duniya a shekarar 2024.
An ruwaito cewa arzikinta ya karu da $15.6bn a wannan shekarar, inda a yanzu ta mallaki $72.3bn. Ta samu dukiyarta daga hannun jarin kamfanin Walmart, da ta gada daga mahaifinta.
1. Françoise Bettencourt Meyers
A lamba ta 1 a jerin mata mafi arziki a duniya ita ce Françoise Bettencourt Meyers, ta kasance tana da shekara 70 a duniya, kuma 'yar kasar Faransa ce.
Dukiyarta ta kai $99.5bn a shekarar 2024, kuma ita ce magajiyar kamfanin L’Oréal wanda ya shahara a samar da kayan kwalliya. Tana rike da kambun mace ta daya mafi arziki na tsawon shekaru hudu.
Jeff Bezos ya fi kowa arziki a duniya
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Jeff Bezos, shugaban kamfanin Amazon, shi ne ya zama mafi arziki a fadin duniya.
An ruwaito cewa arzikin Bezon ya karu sosai tun bayan saukarsa daga mafi arzikin duniya a 2021.
Asali: Legit.ng