Duniya Tayi Sabon Attajirin da Ya Fi Kowa Kudi, An Sha Gaban Elon Musk Mai N180tr
- A duk fadin duniyar nan a yau babu wanda aka sani da ya fi Bernand Arnault yawan dukiya cikin al'umma
- Mujallar Forbes tace baturen na kasar Faransa da danginsa sun mallaki sama da Dala biliyan 207
- Bernand Arnault ya fi Elon Musk mai kamfanin Twitter arziki wanda ake lissafin dukiyarsa ta kai $204bn
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
America - Bernand Arnault da danginsa ba su da tamka idan ana maganar masu kudi yanzu a duniya, har sun zarce Elon Musk.
Mujallar Forbes ta fitar da rahoto, a jerin masu kudin da ke duniya, an hambarar da Elon Musk wanda ya mallaki fam $204.5bn.
Yadda Bernand Arnault ya wuce Elon Musk
Abin da ya faru shi ne kamfanin Musk na Tesla ya gamu da cikas a sakamakon karyewar darajar hannun jarinsa a cikin makon jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A gefe guda kuwa hannun jarin kamfanin LVMH na Bernand Arnault sun tashi da fiye da 13%, hakan ya jawo arzikin danginsa ya karu.
Hannun jarin LVMH sun kai $388.8bn yayin da na Tesla suka gangaro zuwa $586.14bn.
Bernand Arnault da zuri’arsa sun ba $207.8bn baya bayan wani karin arziki da suka samu a ranar Juma’a kamar yadda rahoto ya zo.
LVMH kamfani ne da ya shahara da kayan alfarma, su ne ke da Louis Vuitton da Sephora a yayin da Mista Musk ya saye dandalin X.
Arzikin dangin Bernant Arnault
Arnault yana da yara biyar - Delphine, Antoine, Alexandre, Frédéric, da Jean wanda dukansu suna da matsayi a kamfaninsa.
Ana fargabar mutane 30 sun mutu yayin fada tsakanin sojoji da 'yan bindiga a jihar Arewa, bayanai sun fito
Ratar $3.3bn ne tsakanin manyan attajiran duniyan a yanzu wanda komai yana iya faruwa a cikin ‘yan sa’o’i kadan a duniyar arziki.
Rahoton da aka samu daga jaridar Hindustan Times tace Jeff Bezos ne na uku. A goman farko akwai Bill Gates da Warren Buffet.
Su wanene masu kudin duniya yau?
1. Bernand Arnault
2. Elon Musk
3. Jeff Bezos
4. Larry Ellison
5. Marck Zuckerberg
6. Warren Buffett
7. Larry Page
8. Bill Gates
9. Sergey Brin
10. Steve Ballmer
Bernand Arnault v Elon Musk
A shekarar bara an yi haka, Bernand Arnault ya karbe kambu daga hannun Elon Musk, amma kafin a je ko ina attajirin ya karbe matsayinsa.
Musk mai shekara 52 shi ne ya mallaki kamfanin SpaceX masu kera motocin Tesla Inc da kuma wasu kamfanoni irinsu Neuralink da OpenAI.
Asali: Legit.ng