Ku Taimaka Mun: Yar Najeriya da Ke Karatu a UK Na Neman Naira Miliyan 17.6 Don Biyan Kudin Makaranta
- Omolola Bowoto, wata 'yar Najeriya da ke yin karatun digiri na biyu a jami'ar Essex da ke Ingila, ta na neman taimakon jama'a
- Ɗalibar za ta iya barin makarantar idan ta gaza iya biyan kuɗin karatunta na £20,700 (sama da N23.7 miliyan), yayin da ta shiga shekara ta biyu a jami'ar
- Bowoto ta ce ta tara fam 5,300 (N6 miliyan) don haka tana bukatar ta karasa biyan bashin fam 15,400 (N17.6 miliyan)
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wata daliba ta kafa tsarin 'GoFundMe' domin ta biya bashin kudin makarantar ta yayin da ake daf da korarta daga Jami’ar Essex ta Ingila.
A cikin wani faifan bidiyo na TikTok, Omolola ta bayyana cewa tana shekara ta biyu a jami'ar kuma da wata biyar kadai ya rage mata ta kammala karatun.
Lola ta kara da cewa za ta iya rasa duk wani abu da ta yi na karatun idan aka koreta a halin yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Omolola ta fadi abin da ke kawo tsaiko a tallafin karatunta
Ta shafinta na GoFundMe, Omolola ta ce raguwar darajar Naira da kalubalen iyali ya shafi tattalin arzikin iyayenta, inda ta ce:
“...Saboda faduwar darajar Naira da kalubalen kudi na iyaye ya sa na gaza samun isashen kudin karatuna kuma hakan ya sa na ji takaicin samun kaina a wannan yanayi amma har yanzu ina da kwarin gwiwa na kammala karatuna.
"Ina neman taimakon ku ta kowace hanya da za ku iya bayarwa - ko gudummawar kuɗi, raba wannan sakon neman tallafin a kafofin sadarwar ku, ko da kalamai na ƙarfafawa."
Nawa ne Omolola ta samu tallafi zuwa yanzu?
Yayin da ta yi nuni da cewa ta samu damar tara Fam 5,300 (N6 miliyan) da kanta, Omolola ta bayyana cewa har yanzu ana bukatar Fam 15, 400 (N17.6 miliyan) don kammala biyan kudin makarantar.
Ta yi kira ga masu hannu da shuni da su kawo mata agaji ta hanyar bayar da gudunmawar kudi.
Duba da shafin 'GoFundMe' dinta mai taken 'Taimaki Lola ta kammala karatu a wannan shekarar' ya nuna kawo yanzu ta samu Fam 4,434 (sama da Naira miliyan 5) daga gudummawar mutum 223.
Kalli bidiyon ta a kasa:
An rantsar da Ododo matsayin sabon gwamnan Kogi
A wani labarin, an rantsar da Alhaji Usman Ahmed Ododo a matsayin gwamnan Kogi na biyar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.
Rantsuwar kama aikin tasa na zuwa ne bayan da wa'adin mulkin Yahaya Bello ya kare.
Asali: Legit.ng