Nabeeha: ‘Yan Matan da Pantami Ya Nemowa Kudin Fansa Sun Fito da Aka Biya N100m
- Iyalan Alhaji Mansoor Al-Kadriyar sun samu natsuwa bayan shafe kwanaki kusan 20 a fargaba
- A daren yau ‘yan bindiga suka fito da sauran ‘yan matan da aka dauke tare da Nabeeha a Abuja
- Bayan yin garkuwa da wadannan mutane ne aka kashe Nabeeha, sai da aka biya fansar N100m
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ragowar ‘yanuwan Nabeeha Al-Kadriyah da aka yi garkuwa da su, sun samu ‘yanci kamar yadda muka samu labari.
Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa miyagun ‘yan bindiga sun fito da sauran ‘yanuwan marigayiyar da aka hallaka.
Yaushe aka fito da 'yanuwan Nabeeha?
Da kimanin karfe 12:30 na daren Lahadi aka tabbatar da cewa wadannan Bayin Allah sun kubuta kuma sun isa gidansu a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan za a tuna a farkon Junairu ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ‘yan matan tare da mahaifinsu, suka bukaci a biya su N60m.
An kashe Nabeeha Al-Kadriyah
Daga baya ‘yan bindigan sun kara kudin da suke nema zuwa N100m, kuma suka hallaka guda daga cikinsu, Nabeeha Al-Kadriyah.
Sauran ‘yan matan su ne Najeeba da ke aji 5 da ‘yar uwarta Nadherah wanda ta ke aji uku duk a jami’ar Ahmadu Bello da ke garin Zariya.
Ragowar tagwaye ne Habeeba da Haneesa kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto dazu.
Dangin Al-Kadriyah sun yi jawabi
Da aka tuntubi wani kawunsu, Sherifdeen ya shaidawa manema labarai yaran sun dawo gida bayan kwanaki ana jiran tsammani.
Bayanin Sherifdeen ya tabbatar da ‘yan matan sun samu ‘yanci ne awanni da suka wuce.
A jawabin da ya fito daga Sherifdeen Al-Kadriyah a madadin dangin, ya godewa daukacin ‘yan Najeriya da suka taimaka masu.
Jawabinsa ya ce sun mika babbar godiya ga Allah SWT da addu’a a kan rashin da aka yi, kuma ya jinjinawa matan da aka dauke.
Bidiyon dawowar 'yanuwan Nabeeha
Wani da ake tunanin 'danuwan matan ne, Kabir Aminu ya fito da bidiyon dawowarsu a X.
Nabeeha: Gudumuwar Isa Ali Pantami
Ana da labarin yadda wani abokin Isa Ali Pantami ya bada gudunmawar N50m domin fansar 'yanuwan Nabeeha da ke tsare.
Duk da haka, wannan bai hana miyagun su hallaka wannan Baiwar Allah da kuma wata daliba da ke karatu a jami'ar Bayero ba.
Asali: Legit.ng