Babban Basarake a Najeriya, Abu King Shuluwa Ya Kwanta Dama
- Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Sankera, Abu King Shuluwa rasuwa a asibitin tarayya da ke Makurdi, jihar Benue
- Majalisar sarakunan gargajiya na kabilar Tibi ta fitar da sanarwar mutuwar basaraken a ranar Juma'a
- Rahotanni sun bayyana cewa Sarki Shuluwa ya rasu yana da shekaru 79 a duniya, kuma ya rike mukamai da dama a Benue
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Benue - A ranar Juma’a ne majalisar sarakunan gargajiya na kabilar Tibi (TTC) ta sanar da rasuwar Sarkin masarautar Sankera da ke jihar Benue, Abu King Shuluwa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren majalisar Mista Shinyi Tyozua ya fitar kuma ya bai wa manema labarai a Makurdi.
Sarki Shuluwa ya rasu a asibitin Makurdi
Basaraken, wanda ya kasance Sarki mai daraja ta daya, ya na mulkar kananan hukumomin Ukum, Logo da Katsina-Ala na jihar, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, Tor Sankera, Sarki Shuluwa ya rasu ne a ranar Talata a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Makurdi.
PM News ta ruwaito cewa an haife shi a shekara ta 1946 kuma ya rasu yana da shekaru 79 a duniya.
Takaitaccen bayani game da marigayi Sarki Shuluwa
Kafin rasuwarsa, Abu King Shuluwa shi ne Tor Sankera kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta yankin Sankera kuma mamba a majalisar gargajiya ta yankin kabilar Tibi da majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Benue.
Kafin a nada shi a matsayin sarki mai daraja ta daya, (Tor Sankera) marigayi Sarki Shuluwa an nada shi kwamishina a jihar Binuwai sau uku kuma ya rike wasu mukamai daban-daban, rahoton Daily Trust.
Marigayin dai ya yi takarar kujerar gwamnan jihar sau hudu amma bai samu nasara ba tun a zaben fitar da gwani.
Ango ya mutu ana saura kwana uku auren sa
A wani labarin, wani ango mai suna Abraham Basif ya bakunci lahira ana saura kwana uku daurin aurensa a garin Lokaja, jihar Kogi.
Rahotanni sun bayyana cewa na cikin shirye-shirye ne Basif ya kwanta rashin lafiya, an kai shi asibiti da tunanin zai iya warwarewa kafin ranar auren, amma ajali ya yi kira.
Matar da zai aure mai suna Praise Enyojo ta shiga cikin dimuwa, inda ta ce ba za ta taba samun namiji mai nagartar Basif ba.
Asali: Legit.ng