"Maza 3 da Mata 2": Yar Najeriya Ta Haifi Yara 5 a Lokaci Daya, Bidiyon Ya Dauki Hankula

"Maza 3 da Mata 2": Yar Najeriya Ta Haifi Yara 5 a Lokaci Daya, Bidiyon Ya Dauki Hankula

  • Wata mata ƴar Najeriya ta garzaya yanar gizo domin bayyana yadda ta haifi jarirai biyar a lokaci ɗaya
  • A cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu, an ga matar a wani asibiti, da alama lokacin da ta je domin haifo jariran
  • Ta ce a cikin faifan bidiyon, ta haifi maza uku da ƴan mata biyu, inda ta samu saƙonnin taya murna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata mata ƴar Najeriya ta samu kyautar ƴaƴa biyar, kuma ta bayyana shaidar ta a shafukan sada zumunta.

A cikin wani faifan bidiyo da aka sanya akan TikTok, matar mai amfani da sunan @ebyfullmoon, ta bayyana cewa ta samu ƙaruwar ƴan mata biyu da maza uku.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya aike da muhimmin gargadi ga Gwamna Fubara

Yar Najeriya ta haifi yara biyar a lokaci daya
Yar Najeriya ta cika da murna yayin da ta haifi yara biyar a lokaci daya Hoto: TikTok/@ebyfullmoon
Asali: TikTok

An nuna ta a cikin asibiti tana zagayawa yayin da take gab da haiho jariran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitowar cikinta ya ɗauki hankulan masu amfani da yanar gizo, inda suka yaba mata kan yadda ta iya ɗaukar cikin har na tsawon wata tara.

Ta rubuta a jikin bidiyon:

"Ba zan iya daina gode maka ba Allah, sakamakon ya kasance jarirai biyar, maza uku da mata biyu."

Wane irin martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

@CareTaker ta rubuta:

"A wannan lokacin, ina fatan za mu fahimci ƙoƙarin da mata ke yi... mutum biyar ta ɗauka fa. Ina taya ki murna."

@Ngozi_ca ta rubuta:

"Ina taya ki murna! Ya Allah ka guje ni da irin wannan kyautar. Yara biyar?"

@Angelbby ta rubuta:

"Allah ni kuma mace ce, tagwaye nake so."

@Semzysemzy ya ce:

"Ina taya ki murna. Allah mai iko. Allah ka albarkace ni nima ni da matata. Sama da shekara ɗaya da aure."

Kara karanta wannan

Sojoji sun halaka yan ta'adda 3 da ceto mutanen da suka sace

@Rubystar ta rubuta:

"Na taya ki murna sosai!!!! Kuma ina roƙon ALLAH da ya yi min irin wannan kyautar."

@Bennie_99 ya rubuta:

"Allah sarki...Ta ya kika iya tafiya da yara biyar."

Mata Mai Juna Biyu Ta Haihu a Motar Bas

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mata mai ɗauke da juna biyu ta haihu a cikin wata motar bas da ke tafiya zuwa birnin Warri na jihar Delta.

A cikin wani faifan bidiyo da aka sanya a TikTok, an bayyana cewa matar da abin da ta haifa duk suna cikin ƙoshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng