Kamar Wasa, Masoyin Buhari Ya Rubuta Masa Gayyatar Aure, Kati Ya Isa Gare Shi a Daura

Kamar Wasa, Masoyin Buhari Ya Rubuta Masa Gayyatar Aure, Kati Ya Isa Gare Shi a Daura

  • Tahir Abubakar M. zai zama ango nan da wasu ‘yan kwanaki kadan, bai da gwani irin Muhammadu Buhari
  • Matashin yana rokon Allah SWT ya sa katin daurin aurensa ya iya isa gaban tsohon shugaban Najeriya
  • Da yake Twitter ta tattara jama’a, katin gayyatar zuwa daurin auren Tahir Abubakar ta kai ga Buhari a Daura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Tahir Abubakar M. yana cikin mutanen da ke kaunar Muhammadu Buhari wanda ya yi shekaru takwas yana mulki.

Saboda irin kaunar da yake yi wa tsohon shugaban na Najeriya, Malam Tahir Abubakar M. ya yi burin ya zo daurin aurensa.

Buhari
Masoyi da Muhammadu Buhari Hoto: @mni_JJ
Asali: Twitter

Matashin ya yi magana ne a shafin Twitter, yake cewa yana neman hanyar da takardar gayyatar za ta isa wajen gwaninsa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da kiran a tsige shi, an gano Wike yana rawar wakar Tinubu a ofishin Gbajabiamila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ina katin aure zai je wajen Buhari?

“Na rubutawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari gayyatar zuwa aure na, amma ban wanene ko ta yadda za ta kai gare shi ba.
Na cancanci wasikata ta isa hannunsa, ina bukatar sa albarka da shawararsa.”

- Tahir Abubakar M

Hadimin Buhari ya samu labari

Ba a dade ba, sai maganar ta isa wajen Bashir Ahmaad, wanda shi kuma ya yi shekaru kusan bakwai yana aiki a Aso Villa.

Malam Bashir Ahmaad yana cikin hadiman Muhammadu Buhari a lokacin da yake mulki, kuma har gobe yana haduwa da shi.

Mai ba shugaban kasa shawara a lokacin ya so ya nemi takarar 'dan majalisa a APC.

Katin aure ya kai garin Daura

A karshe dai shi angon na gobe ya aikawa katin gayyatar, da Bashir ya je garin Daura kwanaki, sai ya mikawa tsohon shugaban.

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

A Twitter Mai ba tsohon shugaban Najeriyan shawara ya ce Buhari ya tofa albarka, kuma zai tuntubi Tahir Abubakar daga baya.

Wannan Bawan Allah da ya kammala hada lefen sahibarsa ya godewa Allah SWT, ya ce ba kudi yake nema wajen gwaninsa ba.

Kashe masu maulidi a Najeriya

Kashim Shettima ya ce Gwamnatin da Bola Tinubu yake jagoranta za ta gina gidaje da asibitoci, a taimakawa mutanen Tudun Biri.

Sanata Kashim Shettima ya ce shugaban kasa ya umarci a gina abubuwan more rayuwa a garin da sojoji su ka kashe masu maulidi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng