Soyayyar Sati Daya: Budurwa Ta Tsinci Dami a Kala, Saurayi Ya Tura Mata Makudan Kudade

Soyayyar Sati Daya: Budurwa Ta Tsinci Dami a Kala, Saurayi Ya Tura Mata Makudan Kudade

  • Abin rabo ne yayin da wata budurwa ta baje kolin sakwanni shigar kudi da saurayinta ya tura mata bayan fara soyayyarsu kasa da mako daya
  • Hotunan sun nuna yadda saurayin ke antaya mata kudade akai-akai, inda suka kai dubunnan daruruwa
  • Mutane sun taya buduruwar murna tare da yin mamaki, yadda saurayin ke mata barin kudi duk da ba su haura mako daya da haduwa ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tauraruwar wata budurwa ya fara haskawa a kafofin sada zumunta bayan da ta baje kolin makudan kudaden da saurayinta ya tura mata.

Ko sati daya ba su yi da fara soyayyar ba, amma budurwar ta samu wadannan makudan kudade, lamarin da ya sa jama'a sakin baki cike da mamaki.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Gobara ta yi barna yayin da wuta ta ci hukumar shari’a a jihar Kano

Hotunan makudan kudaden da budurwa ta samu daga saurayin sati daya
Budurwa ta nuna kuɗaden da ta samu daga saurayi a soyayyarsu ta sati daya. Hoto: @jst_pearl1/TikTok.
Asali: TikTok

Budurwar mai suna @jst_pearl1 a shafin TikTok, cikin farin ciki ta rinka nuna hotunan shigar kudade asusunta daga saurayin nata, mutane suka taya ta murna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurwa na murna baki har wuya saboda alkairin saurayi

Makudan kudaden da saurayin ya turawa budurwar abin a yaba ne, la'akari da kankanin lokacin haduwarsu, kowa ya yi mamaki, Legit ta ruwaito.

Hotunan shaidar tura kudin, ya nuna saurayin ya tura mata naira dubu dari 400, naira dubu dari 200, naira dubu 50, naira dubu 25.

Sannan ya tura mata naira dubu 30, naira dubu 35 da kuma naira dubu 20, kuma duka ya tura su ne a lokuta maban-banta.

Wannan tsintar dami a kala da yarinya ta yi, ya bar mutane cikin mamaki, kowa na jinjina irin kyautatawar saurayin a karamin lokaci haka.

Mutane sun nuna mamakin kudaden da saurayin ke turawa budurwar

Kara karanta wannan

"Bana iya ajiye ko kwabo yanzu": Dan Najeriya da ke karbar N200k duk wata ya koka da tsadar rayuwa

Tun bayan da bidiyon budurwar ya zama abin kallo ga dubunnan mutane, an samu ra'ayoyi daga masu tofa albarkacin bakinsu, kan kyaututtukan da budurwar ta samu.

Da yawa na ganin samun saurayi irin wannan, mai barin kudi daga fara soyayya abu ne da sai an tona, irinsu ake kira da tauraro mai wutsiya, ba kowa ke haduwa da shi ba.

@spiffy ta ce :

"Irin haka ta taba faruwa da ni, mako biyu da haduwar mu sai ruwan kudi nake samu, yanzu haka ina gidan saurayin".

@Sarah samuel ta ce:

"Abin mamaki, amma ina fatan dai ni ma Allah bai manta da ni ba saboda irin wannan abin so ne."

@ZEEZAH ACCESSORIES ta yi tsokaci:

"Ya ubangiji ni har sai yaushe?"

@MARAC ta ce:

"Don Allah sanar da ni yana da kani ko yaya?"

@Joy ta ce:

"Ubangiji a duba lamari na"

Duba bidiyon a kasa:

An fasa auren budurwa ana saura sati 2

Kara karanta wannan

Duk da mijina yana kakada min duka, bana son a raba auren mu, mata ta fadawa kotu a Kaduna

Legit Hausa ta kawo maku labarin wata budurwa da ta bayyana bakin cikin da ta shiga bayan an fasa aurenta a watan Disamban 2020

Budurwar mai suna Aderonke ta ce an fasa auren ne saboda matsala da ta samu da 'yar uwar saurayinta

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.