Kyautar Dubu 1 Ga Dalibar da Tafi Kowa Hazaka a Jami'a Ya Girgiza Intanet, Mutane Sun Yi Martani

Kyautar Dubu 1 Ga Dalibar da Tafi Kowa Hazaka a Jami'a Ya Girgiza Intanet, Mutane Sun Yi Martani

  • Abin mamaki ba ya karewa a Najeriya bayan yi wa dalibar da tafi kowa kokari kyautar dubu daya
  • Dalibar mai suna Oluwatimilehin Azeezat ta wallafa kyautar ta naira dubu daya a shafin Twitter da shaidar kyautar daga Jami'ar
  • 'Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda su ke mamakin kankantar kyautar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Budurwa 'yar Najeriya ta girgiza Intanet bayan ta bayyana kyautar da hukumar makaranta ta ba ta a matsayin wacce ta fi kowa shura.

Budurwar mai suna Oluwatimilehin Azeezat Yusuf ta bayyana cewa Jami'ar ta ba ta kyautar naira dubu daya kacal, Legit ta tattaro.

Daliba ta sha mamaki bayan samun kyautar dubu daya a matsayin wacce tafi kowa hazaka a dalibai
Dalibar da tafi kowa hazaka ta samu kyautar dubu daya. Hoto: @yusuf_azeeza.
Asali: Twitter

Mene dalibar ya rubuta a shafin Twitter?

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan wasu ‘yan bindiga sun bindige shugaban jam’iyyar siyasa a jihar Anambra

Azeezat ta wallafa hotonta a shafin Twitter inda take murnar kammala karatu a Jami'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubutu kamar haka:

"Ku kira ni da Dakta Baby da ta tashi da kyauta.
"Ku tayani murnar kammala karatu."

A wallafawarta ta hada da wata takarda da ke dauke da kyautar dubu daya da Majalisar makarantar ta amince a ba ta.

Budurwar ta samu kyautar ce da sahalewar tsangayar da take karatu a Jami'ar.

'Yan Najeriya sun yi martani kan wannan lamari inda suke ke mamakin irin wannan kyauta.

Wane martani 'yan Najeriya su ka yi kan kyautar?

@bukolayoola:

"Dubu daya ko miliyan daya?
"Ina bincike don gano gaskiya, watakila kuskure ne."

@adeseun4u2c:

"Akwai matsala a yadda aka rubuta lambobin."

@darcsensation:

"Na taya ki murnar kammala karatu."

@iOh Jay:

"Na taya ki murna Azeezat, zan so na san yadda zaki kashe wadannan makudan kudade da kika samu."

Kara karanta wannan

Umar Ka'oje: Farfesan Najeriya ya mayar da fiye da miliyan 1 da aka tura masa bisa kuskure

Matashi ya kona takardun karatunsa tun daga firamare

A wani labarin, wani fusataccen matashi ya cinna wa takardun karatunsa wuta tun daga firamare har zuwa Jami'a.

Matashin mai suna Lanre ya ce satifiket din ba su da amfani a wurinsa tun da ya shafe shekaru 13 babu aikin yi a Najeriya.

Mutane da dama sun yi martani yayin da wasu ke yabon shi wasu ko cewa suke ya tafka kuskure saboda ba takardu ke ba da arziki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel