Abin da Mahaifinmu Ya Fada Mani Game da Sirrin Kasuwanci Inji Aminu Dantata

Abin da Mahaifinmu Ya Fada Mani Game da Sirrin Kasuwanci Inji Aminu Dantata

  • Aminu Dantata ba haka nan ya yi kudi ba, danginsa sun gaji kasuwanci shekaru da-dama, har gobe ana cikin dukiya
  • A wata hira da ya yi kwanaki, attajirin ya bada labarin yadda ya fara neman kudi har ya mallaki biliyoyi a gida da waje
  • Kafin mahaifinsu Alhasan Dantata ya rasu, ya ba su shawarar su mallaki filaye domin akwai riba a kasuwancin kasa

Kano - A wata hira da aka yi da shi, abin da ba a saba ji ba, Aminu Dantata ya yi magana game da gidansu, tarihin rayuwarsa da kasuwancinsa.

Alhaji Aminu Dantata ya ba Daily Trust damar tattaunawa da shi kuma ya amsa tambayoyi tun daga tashinsa zuwa yanzu da ya yi fice a duniya.

Tun su na yara, Dantata ya ce mahaifinsu ya koya masu neman arziki, ya fara da zubawa rakuma, dawaki da jakuna ruwa domin samun 'yan taro.

Kara karanta wannan

'Yan Siyasa 5 Masu Neman Shugaban Kasa da Tinubu Ya Bai Wa Mukami a Gwamnatinsa

Aminu Dantata
Alhaji Aminu Dantata Hoto: @Musaddiqww, @MaiturareAbdoul
Asali: Twitter

Dantata ya dade da fara neman kudi

"A gidanmu daga shekaru bakwai ko takwas, mahaifimu ya fara nuna mana neman kudi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Aminu Dantata

Kafa kamfanin Al Hassan Dantata & Sons

Kafin rasuwar mahaifinsa Alhaji Al Hassan Dantata, sai ya kafa kamfanin Al Hassan Dantata & Sons, jim kadan bayan nan kuma rai ya yi halinsa.

Ahmadu Dantata ne ya fara zama shugaba, daga baya aka rabu zuwa kamfanin Al Hassan Dantata & Sons da kuma kamfanin Sanusi Dantata.

A shekarar 1947, Dantata mai shekara 92 ya canji ‘danuwansa watau Marigayi Ahmadu Dantata a kasuwancinsu

Dattijon da danginsu sun yi fice ya fadawa jaridar bayan rasuwar ‘danuwansa sai Garba Maisikeli ya karbi ragamar kamfanin, ya na mataimaki.

Aminu Dantata ya san darajar filaye

"Da mu ke girma, sai na fara kokarin koyi da mahaifina wajen sayen filaye. Ya yi ta fada mana, “idan ku na neman kudi, ku mallaki filaye."

Kara karanta wannan

Malamin Addini Ya Hango Gagarumin Matsala a Jihar Ondo, Ya Ce Gwamna Akerodlu Na Bukatar Addu'a

- Aminu Dantata

Ganin cewa an yi masa tarbiyyar sayen filaye, attajirin ya ce ya mallaki filaye a Kano da garuruwan fadin kasar nan da kuma kasashen waje.

‘Dantata ya na da filaye a Saudi Arabia, Dubai, Dubai, Masar, Jamus har da gida a birnin Florida a Amurka inda ‘ya ‘ya da jikokinsa ke karatu.

Alhaji Aminu Ɗantata ya yi rashi

Kwanakin baya aka samu labari cewa attajirin ɗan kasuwa, Aminu Ɗantata, ya yi rashi, wata a cikin dangin Alhasawa ta riga mu gidan gaskiya.

Ɗaya daga cikin jikokinsa mai suna, Batulu, ta rasu tana da shekaru 40 a duniya. Ana da labari ta rasu ne bayan fama da cutar sikila na tsawon lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng