Aminu Dantata ya cika shekaru 90: Ga wani balli daga cikin tarihinsa

Aminu Dantata ya cika shekaru 90: Ga wani balli daga cikin tarihinsa

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dantata, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya cika shekaru 90 a duniya a yau Laraba, 19 ga watan Mayu.

Tun daga yarinta har zuwa zama babban hamshakin attajiri kuma mashahurin mai taimakon jama'a, an haifi Alhaji Aminu a ranar 19 ga Mayu, 1931, a cikin gidan Alhassan Dantata.

A ranar 15 ga Afrilu, 2021, Alhaji Aminu yana daga cikin fitattun mutanen Kano, ciki har da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wadanda suka sulhunta Alhaji Aliko Dangote, Shugaban rukunin kamfanin Dangote, da Abdussamad Isyaka Rabi’u, Shugaban rukunin kamfanin BUA.

Irin wannan karimcin, kimanin wata daya kafin ya cika shekaru 90, ya tabbatar da shi a matsayin sanannen mai son zaman lafiya.

Aminu Dantata ya cika shekaru 90: Ga wani balli daga cikin tarihinsa
Aminu Dantata ya cika shekaru 90: Ga wani balli daga cikin tarihinsa Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: 2023: Hotunan Neman Takarar Sanata na Gwamna Ortom Sun Mamaye Makurdi

Tsohon kirkin ya yi karatunsa na sharer fage daga 1938 zuwa 1945 a makarantar Firamare ta Dala, kuma ya halarci Makarantar Turanci da Larabci ta Dantata tsakanin 1945 da 1949.

Mahaifinsa, Alhassan Dantata, an haife shi a shekara ta 1877 kuma ya mutu a watan Agusta 17, 1955, ɗan kasuwa ne a fannin kayayyakin amfanin gona, wanda ke tallata hajarsa har a ƙetaren Najeriya.

Dantata karami ya yi saurin koyi da kasuwancin mahaifinsa kuma ya yi fice sosai a fagen kasuwancin.

Harkokin kasuwancinsa

Ya fara harkokinsa a matsayin mai siyen kayayyaki a 1949 a kasuwancin dangin Alhassan Dantata and Sons Limited, ya zama Shugaba kuma Manajan Daraktan Kamfanin a 1960.

Ya kasance memba na Kwamitin Gudanarwa na Bankin bunkasa Masana'antu na Najeriya (yanzu Bankin kasuwanci), ya kuma zama Daraktan Bankin tsakanin 1962 da 1966.

Alhaji Aminu Dantata shi ne wanda ya kafa kamfanin Express Petroleum and Gas Company Limited kuma yana daga cikin mutanen da suka jagoranci Bankin Jaiz a Najeriya.

Fitaccen dan kasuwar ya shaida wa jaridar Daily Trust a bara lokacin da ya cika shekaru 89 cewa tun daga 1956, ya ziyarci duk wata babbar kasa a duniya, ciki har da su Australia, Indiya, China, Brazil, Yugoslavia, Russia da duk kasashen Larabawa da Isra'ila.

Abu mafi muhimmanci, ya jagoranci ayyukan kasuwanci da yawa zuwa ƙasashe da yawa a duk faɗin duniya.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram na amfani da damar annobar korona wajen dawowa Najeriya, Buhari

A matsayinsa na wanda ya kafu a harkar kasuwanci, Alhaji Aminu Dantata ya yi imanin cewa kasuwanci yana da maganin rashin zaman lafiya da rashin aikin yi kuma ya bayyana hakan ne a cikin maganganunsa na baya.

"Daga kasuwanci za ku samu masana'antu kuma mutane za su sami kwanciyar hankali a harkokin kasuwancinsu, kuma shugabanni za su mallaki talakawansu kuma su bunkasa al'umma a dukkan matakai," kamar yadda ya fada wa Daily Trust.

Dantata a Siyasa

Yayin da aka fi sanin Alhaji Aminu da manyan nasarorin da ya samu a fagen kasuwanci, ya kuma jefa ƙafafun sa a harkar siyasa a Najeriya kasancewarsa ɗan majalisar wakilai na lokaci ɗaya a Kaduna a lokacin Jamhuriya ta Farko, sannan kuma ya kasance mamba a majalisar lardin Kano.

Ya kuma taba rike mukamin mamba na sabuwar Jihar Kano da aka kafa a shekarar 1967, inda ya yi aiki a matsayin kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar a karkashin marigayi Audu Bako, gwamnan Kano a lokacin gwamnatin soja ta Janar Yakubu Gowon.

Gabanin Jamhuriya ta Biyu, wacce ta samar da marigayi Alhaji Shehu Shagari a matsayin shugaban kasa, Dantata ya tuno da kiraye-kiraye da wasu fitattun mutane suka yi na ya nemi takarar shugaban kasa.

Mutum mai kyawawan ɗabi'u ya bayyana dalilinsa na ƙi amsa kiran da aka yi: “Dalilina na ƙin waɗannan tayin mai sauƙi ne. A matsayina na dan kasuwa da ke da manyan ayyuka, na yi imani Allah Ya riga Ya zaba min sana’a, ta inda zan taka rawa na don ci gaban jiha ta, kasa ta da ma bil’adama baki daya.”

Mutum mai tarin yara da jikoki, Dantata ya yi imanin cewa ya kamata ayi la’akari da hada ilimin Islama da na boko a Arewacin Najeriya ba wai kawai a ilimantar da matasa ba, amma a duba lalacewar tarbiyya a cikin al’umma.

Yaki da lalacewar dabi’u abu ne da ya rataya a wuyan kowa, musamman gwamnati, malaman addinin Musulunci, sarakunan gargajiya, manyan ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma, wadanda ya shawarce su da su hadu domin ceto kasar tun kafin lokaci ya kure.

Ra'ayoyinsa game da magance lalacewar ɗabi'a

Don magance tabarbarewar kyawawan dabi'u a cikin al'umma a yau, ya ce, "ya kamata canjin ya fara ne daga gidajenmu, makarantu, wuraren aiki da kasuwanninmu. Abin takaici ne matuka cewa kyawawan halaye a hankali suke bacewa, musamman a tsakanin samarinmu. Kuma har sai mun magance wannan, ba za mu taba samar da shugabanni masu nagarta na gaba ba ”.

Dattijon ya damu da tsarin ilimin Najeriya kuma ya yi magana game da bukatar inganta tsarin ilimin kasar.

“Idan ka tantance kayan jami’o’inmu a yau za ka yi imani da cewa mu yaye dalibai da basu nuna ba. Yawancinsu suna da ilimin amma ba su da kyawawan halaye,” kamar yadda ya shaida wa jaridar a wata tattaunawa.

Wata matsalar da ke ci wa dan kasuwar tuwo a kwarya shi ne rufe masana’antu tsakanin Kano da Kaduna, wanda hakan ya haifar da asarar daruruwan ayyuka.

Shahararren dan kasuwar ya shaida hakan ko a kwanan nan lokacin da ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 300 ga Kwamitin tara Kudi a kan COVID-19 a Jihar Kano da Gwamna Ganduje ya kafa.

Shekarun baya, ya ba da gudummawar Naira miliyan 500 don kammala Masallacin Kasa da ke Abuja.

Ayyukan al'umma

Wani tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya taba bayyana cewa Alhaji Aminu Dantata ya kammala ayyukan da suka kai kimanin naira miliyan 400 a fadin jihar ta Kano.

A shekaru 90, yayin da a bayyane yake cewa Alhaji Aminu ya fara ja baya a harkar kasuwanci ta hanyar barin yaranshi su dauki manyan ayyuka a rukunin kamfanonin iyalan, da kyar gogaggen dan kasuwar zai bar wurin gaba daya saboda lokaci.

Ana kallon sa a matsayin daya daga cikin mawadata mafi alkhairi a Najeriya, wanda kyautatawarsa ya canza rayuwar mutane da dama.

A lokacin da yake zuba jari a matsayinsa na Shugaban Jami’ar Musulunci ta Katsina, ya bayyana abin da ya haifar da ayyukan alherinsa a rayuwa: “Ya ku‘ yan’uwa maza da mata, ina so in tunatar da ku wani muhimmin aiki da Allah Madaukaki Ya ɗora mana. Wannan nauyin shi ne ciyar da mabukata gaba daya.”

Dangane da dukiyar da ya samu a rayuwa tsawon shekaru, ya ce, “Allah ya wajabta wa masu hannu da shuni su ba da taimako ga mabukata ta hanyar bayar da umarni kai tsaye da su bayar daga abin da (Allah) ya ba su kamar yadda umarnin Musulunci ya tanada.

Duk da yawan shekarunsa, Alhaji Aminu ya bayyana a wata tattaunawa da Daily Trust a bara cewa har yanzu yana la’akari da sabbin harkokin kasuwanci kuma ba abin mamaki ba ne ka ga yawancin kasuwancin da ke bunkasa da sunansa a makonni masu zuwa, watanni da shekaru kamar yadda yake ci gaba more rayuwa zuwa gaba.

A wani labarin, kakan mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, yana daya daga cikin 'yan Najeriya da suka fara amfani da banki bayan da aka bude shi.

Kamar yadda wani tsohon rasit ya nuna wanda Nigeria Stories ta wallafa a shafinta na Twitter, dan kasuwan ya zuba kudin ne yayin da aka bude Bankin Turawa wanda yanzu shine First Bank karon farko a jihar Kano a shekara 1929.

Ko a wancan lokacin, Alhaji Alhassan Dantata ya nuna tsabar kudinsa kuma ya tabbata babban attajiri. Ya laftawa rakuma 20 sisin azurfa inda suka kai bankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng