An Kori Annie Knight Daga Wurin Aiki da Aka Gano Ta Kwanta da Maza Sama da 300
- Idan ana maganar matan da su ka yi suna a Onlyfans a duk duniya, watakila ba za a rasa kawo irinsu Annie Knight ba
- Wannan mata mai shekaru 26 a duniya ta kan yi lalata da mazaje dabam-dabam a rana, adadin ya kai 300 a shekara
- A yayin da wurin da ta ke aiki su ka gano sirrin Annie Knight, ba su yi wata-wata ba, sai su ka kore ta daga bakin aiki
Australia - Annie Knight ‘yar kasar Australiya mai shekaru 26 ta rasa aikinta a sakamakon gano asirinta da aka yi a shafin OnlyFans a ofis.
Daily Mail ta ce an kori Annie Knight wanda ta na cikin wadanda su ka fi kowa shahara a dandalin OnlyFans saboda lalata daga wurin aiki.
A ranar Talata wannan mata ta bada labarin abin da ya faru a SBS’ Insight, ta na cewa ta yi mamakin yadda aka sallame ta daga aikin na ta.
Annie Knight ta rasa aikinta
Annie Knight ta ce ko da ta fara amfani da OnlyFans, hankalinta bai kwanta ba, amma ba ta yi tunanin za ta rasa hanyar neman abincinta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kwarai, wannan shi ne abin da ya fi damu na lokacin da na fara bude akawun din.
"Abin da ba zan taba so ya faru ba shi ne a kore ni idan wani ya gano ni a OnlyFans.
"Ban dade da fara sabon aiki na ba. Rana na biyar kenan, na je gida saboda rashin lafiya a ranar, sai ga imel cewa an fatattake ni daga aiki."
- Annie Knight
Asirin Annie Knight a OnlyFans ya tonu
Punch ta ce a sakon imel da aka aiko mata, an nuna mata hoton shafinta da kuma wasu dalilai uku da su ka jawo ta rasa hanyar samu.
Abin da watakila ya yi wa Knight kuna shi ne ta na samun kudi fiye da yadda ta saba a sabon aikin da aka dauke ta, sai ba a je ko ina ba.
Mace mai lalata da tulin maza
Kwanaki aka yi hira da Knight a shirin The Kyle and Jackie O inda ta yi bayanin yadda ta ke tunkaho da kwana da mazaje 300 a shekara.
A duk rana, sai ta samu alaka da maza biyar da ba ta san daga inda su ka fito ba, babu inda Knight ba ta tarawa da masoya – a gida ko waje.
Mutuwa rigar kowa
A gida Najeriya, a yau aka samu labarin mutuwa ta ratsa Majalisar tarayya a karon farko cikin watanni hudu a sabuwar gwamnatin kasar.
Hon. Abdulkadir Jelani Danbuga mai wakiltar Isa-Sabon Birni ya rasu bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita a asibiti a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng